Hukumar ‘yan sandan Nijeriya ta bayyana zargin cewa, faɗuwar wasu ƙananan yara masu laifi da aka gurfanar a babbar Kotun tarayya da ke Abuja a ranar Juma’a kan zanga-zangar ‘End Bad Governance’ ta watan Agustan 2024, a matsayin “wasan kwaikwayo da aka tsara.”
Rahoton News Point Nigeria ya nuna cewa hukumar ‘yan sandan ta yi wannan martanin ne bayan wasu daga cikin waɗanda ake zargi da aka gurfanar suka faɗi a gaban Mai shari’a Obiora Egwuatu.
Masu laifin, guda 75, da shekarunsu suka kama daga 12 zuwa 15, an tuhumesu da tuhume-tuhume 10 da suka haɗa da ta’addanci, yunƙurin kifar da gwamnati, da kuma tayar da zaune tsaye saboda rawar da suka taka a zanga-zangar ƙasa baki ɗaya.
A ranar 3 ga watan Agusta ne aka cafke su, kuma tun daga lokacin suna tsare. Sai dai kuma yayin ƙorafe-ƙorafe da ke bibiyar wannan gurfanar, hukumar ‘yan sanda ta bakin Kakakin ta, ACP Olumiyowa Adejobi, ta ce wannan “lamari da aka gani na faduwa ba zato ba tsammani a kotu, wani yunƙuri ne da aka shirya don jawo hankalin kafofin watsa labarai da kuma zubar da mutunci.”
Hukumar ta bayyana cewa ta yi duk mai yiwuwa wajen tabbatar da adalci da bin doka a tsarin tsarewa da gurfanar da waɗanda ake zargi. Haka kuma, ta tabbatar da samun kulawar lafiya da sauran haƙƙoƙi ga duk wanda ke tsare a hannun hukuma, ba tare da la’akari da zargin da ake musu ba.