Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
A Nijeriya, wasu daga cikin sojojin ƙasar da ke ayyukan samar da tsaro a jihar Zamfara sun koka game da yawan jinkirin da ake samu, wajen biyansu kuɗaɗensu na alawus, inda suka ce akan biya su kuɗin wata guda ne kacal bayan kwashe watanni biyu ko uku, lamarin da ke jefa su cikin halin ƙaƙa-ni-ka-yi a cewarsu.
Sai dai hukumomin sojan Nijeriyar sun ce suna sane da wannan ƙalubale da ke gaban dakarun da ke fagen daga, amma ana ƙoƙarin shawo kan lamarin nan ba da daɗewa ba.
Wasu sojojin da suke aiki ƙarƙashin rundunar Operation Hadarin Daji a jihar ta Zamfara, ne suka shaida wa BBC ƙorafin nasu.
Sun bayar da misali da cewa, sai a ranar Litinin ta wannan mako aka fara biyansu alawus na watan Mayun da ya gabata.
Har ma sun fara bayyana fargaba, cewa mai yiwuwa kafin a biya su alawus na watan Yuni sai cikin watan Satumba mai zuwa.
Sun ce akwai ma waɗanda daga cikinsu har yanzu ba a ma biya su alawus na watan Maris ba.
Sojojin da ke fagen dagar sun bara, cewa tsaikon biyansu alawus na jefa su cikin tsaka-mai-wuya.
Dangane da waɗannan ƙorafe-ƙorafe dai, BBC ta tuntuɓi Guruf Kyaftin Ibrahim Ali Bukar, mataimakin daraktan watsa labarai na hedikwatar tsaron Nijeriyar, inda ya yaba da irin ƙoƙarin da dukkan jami’ansu suke yi wajen yaki da ‘yan ta’adda.
Sannan ya ce: “Shugaban sojoji Janar Christopher Musa, zai yi duk abin da zai yiwu domin ganin an kyautata masu, kuma su ci gaba da samun nasarori a daƙile ‘yan ta’adda, dangane da matsaloli da ake fuskanta, ana kan yin abin da ya dace, da zaran babban bankin Nijeriya ya kammala aikinsa kowa zai samu abinshi, Insha Allah.”
Guruf Kyaftin Ibrahim Ali Bukar ya ce Janar Christopher Musa ya yi kwamandan yaƙi saboda haka ya san dukkan matsalolin da ke tattare da soja a daji, “Kowa zai samu kuɗinsa kai tsaye ta asusun bankinsa saboda haka ake yi.”
Ƙorafin na tsaikon biyan alawus ga dakarun Nijeriya da ke fagen daga dai, ba wai a jihar Zamfara kaɗai ya tsaya ba, domin kuwa binciken da BBC ta gudanar ya nuna cewa, abin yana nema ya zama wani ruwan dare a ƙasar.
Al’amarin da masana harkokin tsaro ke ganin yana iya shafar karsashin dakarun, idan har ba a hanzarta yi wa tufkar matsalar hanci ba.
