Wata ƙungiyar Dattawan Arewa ta yaba wa sojin Nijeriya kan yadda kwalliya ke biyan kuɗin sabulu

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Wata ƙungiyar dattawa mai rajin kawo cigaban siyasa a Arewa (Northern Elders Political Development Group) ta ce inganta tsaro ya dawo da al’umma yankin Arewa ƙarfin guiwar da suke da shi na samun zaman lafiya.

Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar a Kaduna ta hannun sakatarenta, Dr Adamu Giwa.

Kamfanin Dillancin Labarai na ƙasa NAN ne ya rawaito cewa a watan Oktobar 2024, gwamnatin tarayya ta ƙaddamar da wata runduna mai suna “ofureshan fansar yamma” wacce za ta tunkari matsalar tsaro da kawo ƙarshensa a yankin Arewa maso yamma.

“Matakan da rundunar ofureshan fansar yamma suka ɗauka ya tabbatar da alƙawarin da shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ya yi na ganin kyakkyawar sakamako na raguwar ayyukan ‘yan bindiga da satar mutane da ake yi a ƙauyuka da ake yankin,” a cewar ƙungiyar.

ƙungiyar ta yaba wa ƙaramin ministan tsaro, Mohammed Matawalle da shugaban hafsan tsaro, janar Christopher Musa, kan haɗin kansu wajen yaƙi da matsalar tsaro a yankin Arewa maso yamma.

“Da yawan ƙauyuka da ke yankin nan sun gudanar da sallar Idi cikin ƙoshin lafiya ba tare da labarin wani harin ‘yan bindiga ba.”

“Sannan muna yaba wa rundunar sojin Nijeriya da ke ƙarƙashin rundunar ofureshan fansar yamma waɗanda suka fatattaki ‘yan bindiga daga maɓoyarsu a wasu yankuna na Arewa maso yamma.”

Ingantuwar tsaron muhimmin abu ne ga harkokin tafiye-tafiye da kasuwanci, musamman tsakanin hanyoyin da suka haɗa Kano da Sakkwato da Gusau,” inji ƙungiyar.

“Dabarun kai samame wuraren da ‘yan bindigar ke fakewa da rundunar ke yi babbar nasara ce,”

“Duk da ba kai ga ƙarar da su ba bakiɗaya, amma mun yi imani cewa ana kan hanyar da ta dace wajen kakkaɓe su.”

Sai dai ƙungiyar ta yi jan hankali ga yawan samun rahotannin saukar bam a wasu ƙauyuka da aka samu a Sabon Birni da Isa, da ke Sakkwato da ƙarin wasu ƙauyukan a jihohin Katsina da Kebbi da Zamfara.

By ukarofi