Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Hukumar Shige da Fice ta ƙasa (NIS) ta kama wasu mutane 51 da ake zargin sun ‘yan asalin ƙasar Mali ne da suka shigo ba bisa ƙa’ida da ke zaune a Sabuwar Nyanya a ƙaramar Hukumar Karu ta jihar Nasarawa.
Sabuwar Nyanya ɗaya ce daga cikin unguwanni da ke kusa da babban birnin tarayya Abuja.
Sanarwar kama mutanen na cikin wani sako da jami’an yaɗa labarai na hukumar, Akinsola Akinlabi, ya fitar a ranar Laraba a Abuja.
Mista Akinlabi ya ce, binciken farko-farko ya nuna matafiyan na iya kasancewa an yi safararsu ne zuwa Nijeriya.
Ya ce ba a same su da wasu takardu ingantattu na tafiye-tafiye ba, kuma ba wata takarda da ke nuna inda suka fito.
A cewarsa, an kama su ne a ranar Litinin bayan samun bayanan sirri.
“Waɗanda aka kama ɗin, akwai mata 11 da maza 40 da suke tsakanin shekaru 16 da 19.”
“Kuma tuni aka wuce da waɗanda aka kama zuwa ofishin hukumar domin gudanar da bincike a kansu.”
“Za mu yi ƙoƙarin gano dalilin shigowa Nijeriya da suka yi da alaƙarsu da safarar mutane ko fasaƙauri,” ya faɗa.
Mista Akinlabi ya ce, hukumar za ta cigaba da himmatuwa wajen tabbatar da tsaro a iyakokin Nijeriya daga kwararowar mutane ba bisa ƙa’ida ba da kare haƙƙin waɗanda suka bi ƙa’ida.
Ya ce hukumar za ta cigaba da aiki da masu ruwa da tsaki domin yaƙi da masu safarar mutane yadda ya kamata.
Mai magana da yawun hukumar ya ba da tabbacin cewa hukumar a shirye take wajen tabbatar da tsaro da kula da shige da ficen mutane a Nijeriya.
Ya kuma yi kira ga al’umma da su ba da rahoton duk wani da ya shafi kwararar mutane ga ofishin hukumar mafi kusa.
