Wata mata ta fashe da kuka bayan dangwala wa Tinubu ƙuri’a bisa kuskure

Daga AISHA ASAS

An hango wata mata a mazaɓa mai lamba 047 da ke unguwar Kubwa, a rumfar makarantar firamare da ke cikin birnin tarayya Abuja, tana tana rusar kuka, sakamakon abinda ta kira da tsautsayi da ya afka mata ta hanyar jefa ƙuri’arta ba a inda ta yi niyya ba.

Kamar yadda ta faɗa, ta dangwala wa Asiwaju Bola Tinubu, amma fa bisa ga kuskure, domin ba shi ne ta yi niyyar zaɓa ba.

Iya ƙoƙari an yi na samun ƙarin bayani daga bakin wannan baiwar Allah kan yadda lamarin ya faru tare kuma da sanin dalilin faruwar wannan kuskure, sai dai ta tabbatar da cewa, ba za ta yi magana da manema labarai ba.