An cinna wa ofishin INEC na Takai wuta a Kano

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Hukumar ‘yan sanda a Jihar Kano ta tabbatar da cewa an cinna wa ofishin Hukumar Zaɓe na Nijeriya reshen Ƙaramar Hukumar Takai wuta.

Kakakin rundunar SP Abdullahi Haruna kiyawa ne ya tabbatar wa da manema labarai faruwar lamarin.

‘Yan banga ne suka cinna wa janareton da ake aiki da shi a cibiyar wuta, lokacin da suka shiga wajen ta baya, amma ba wani ci ta yi ba, kuma an kashe ta, tuni muka ƙara yawan jami’anmu a wajen,’ inji Kiyawa.

Manhaja ta tuntuɓi wani ganau wanda ya ce an cinna wutar kuma ta ƙona wasu robobi da aka zuba takardun ƙuri’un da aka kaɗa amma ba ta ƙona wajen da ake aikin ƙirga ƙuri’u ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *