WHO ta shirya wa ‘yan jarida taron ƙara wa juna sani a Yobe

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN, Damaturu

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) da haɗin gwiwa da Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Yobe, sun shirya taron ƙara wa juna sani na kwanaki uku a ranar Laraba ga ‘yan jarida haɗi da masu hulɗa da kafafen sada zumunta (Social Media Influencers) domin samun horo wajen bayar da sahihan rahotanni kan ɓarkewar annobar cututtuka masu saurin yaɗuwa.

Taron bayar da horon yana gudana ne a babban ɗakin taro da ke ‘Sand Dune Hotel’ a Damaturu, babban birnin Jihar Yobe; wanda ya samu halartar ‘yan jarida da masu hulɗa da kafafen sada zumunta daga kowane ɓangaren jihar.

Da yake jawabi a wajen taron, Kodinatan Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) a Jihar Yobe, Dr. Ningi Barau ya bayyana cewa, maƙasudin shirya horon shi ne domin karkato da tunanin jama’a zuwa samun sauyin dabi’u dangane burin da ake da shi a fannin bunƙasa harkokin kiwon lafiyar al’umma a Jihar Yobe.

Dr. Ningi ya kara da cewa, muhimmancin yada labaru tare da sahihan bayanai abu ne mai matuƙar alfanu wajen dakile kowace barazana ta bazuwar annobar cutuka masu saurin yaɗuwa idan sun barke.

“Saboda idan ba a wayar da kan jama’a ba dangane da irin wadannan cutukan ba; musamman yadda ake kamuwa dasu, ko kuma yanayin cutukan, da matakan da ya dace su ɗauka idan sun kamu, ka ga kenan akwai ɗimbin matsaloli.

“Saboda zai yuwu mutane su harbu da cuta ba tare da sun sani ba, alhalin ita kuma cutar zata yi ta bazuwa, ta fantsama cikin mutane bila adadin, al’amarin da ka iya kaiwa ga rasa rayuka da dama,” In ji Kodinatan WHO na Yobe.

Sa’ilin da yake karin haske dangane da makasudin shirya horon, daya daga cikin ma’aikatan hukumar WHO, Mr Kingsley Igwebuike, ya jaddada cewa taron zai taimaka wajen bunƙasa ilimin mahalartan ba a fannin bayar da rahotanni kaɗai ba.