Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Ministan Babban Birnin Tarayya, Abuja, Nyesom Wike, ya janye dukkan lasisin wuraren shaƙatawa da ke Abuja, inda ya umurci mamallaka wuraren da su sake miƙa takardunsu domin tantance yiwuwar sake musu sabbin wurare.
Daraktan Sashen Kula da Ci Gaban ƙasa Murkhtar Galadima ne ya bayyana haka a wata hira da manema labarai a ranar Alhamis yayin da yake bayyana dalilan rushe garejin Bouleɓard da ke Maitama a Abuja.
Ya ce, hukumar ta shirya rusa wani katafaren wurin da ke gundumar Durumi inda wasu miyagu ke fakewa da sunan ‘yan gudun hijira.
Galadima ya ƙara da cewa, ministan ya ɗauki matakin janye dukkan lasisin ne biyo bayan wata takarda da daraktocin wuraren shaƙatawa suka gabatar a haɗe, wanda ya nuna gazawa da kuma cin zarafi da ke tattare da gudanar da wuraren shaƙatawa a yankin.
Galadima ya ce, sabon umarnin ya baiwa masu gudanar da wuraren shaƙatawa damar sake miƙa takardunsu ga sashen shaƙatawa domin dubawa.
“Idan sun cika sharuɗɗan, za a iya sake mayar da su. Masu gidajen shaƙatawa su amsa kiran, su miƙa takardunsu, kuma idan sun cika sharuɗɗan, za su koma wuraren shaaatawa nasu,” inji shi.
