
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ƙungiyar Likitoci ta Ƙasa (NARD) ta shiga yajin aikin gargaɗi na kwanaki biyar domin matsa wa gwamnati akan buƙatunta.
Sakatare Janar na NARD, Dakta Oluwasola Odunbaku ya sanar da haka ta kafar X a jiya Juma’a.
Ƙungiyar ta ɗauki matakin ne bayan matsaya da majalisar zartarwarta ta cimma a wani zama da ta gudanar bayan da wa’adin da ta ba Gwamnatin Tarayya akan buƙatun nata na 10 ga watan Satumba, 2025 ya ƙare.
Don haka ta sanar da ɗaukacin mambobinta a faɗin Nijeriya da su fara yajin aikin a yau, wanda za a ɗauki tsawon kwanaki biyar ana yi.
Ta kuma yi kira ga mambobin nata da su tabbatar da kiyaye umarnin a ko’ina suke a Nijeriya.
NARD ta bayyana cewa, ta yi haka ne domin gwamnati ta amsa buƙatun walwalarsu na tsawon lokaci, da suka haɗa da inganta wuraren aiki da bunƙasa cibiyoyin lafiya ga al’ummar Nijeriya.
Shugaban ƙungiyar, Dakta Tope Osundare ya shaida wa Daily Post cewa sun tafi yajin aikin ne sakamakon rashin kyan wuraren aiki, rashin wadataccen wutar lantarki, rashin daraja takardunsu na matakan karatu, rashin wadataccen albashi da dai sauransu.
