Yadda Temi Otedola ta canja sunan attajirin mahaifinta zuwa na mijinta

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Temi Otedola, ɗiyar hamshakin attajirin ɗan kasuwa, Femi Otedola, ta yi watsi da sunan mahaifinta domin ɗaukar sunan mijinta, Mista Eazi.

Temi Otedola ta tabbatar da ci gaban ga kowa da kowa a ranafr 5 ga Satumba, 2025 ta shafin ta na Instagram, inda ta canja sunanta daga Temi Otedola zuwa Temi Ajibade.

Mijin nata ya kasance shahararren mawaƙin Nujeriya kuma marubucin waƙa, Eazi.

A shekarun baya, fitaccen hamshaain mai kuɗi a Nijeriya, Femi Otedola, ya bayyana yanayin ƙaunar da yake yi wa ‘ya’yansa mata uku.

Biloniyan babu shakka uba ne mai ƙaunar ‘ya’yansa domin kuwa cikin kwanakin nan ya fitar da ‘ya’yansa sayayya inda ya kashe musu miliyoyin kuɗi domin sayen motoci.

Otedola ya saya wa kowacce ɗiyarsa mota ƙirar Ferrari Portofino. ‘Ya’yansa da ya saya wa motocin sune Temi, Tolani da DJ Cuppy.

Ya saya musu motar sabuwar fitowa ta shekarar 2020 wacce ake cewa tana da tsananin gudu. Ana siyar da kowacce daya a kan kuɗi miliyan N82.2.

Motocin sun zo a launikan da kowacce ɗiyarsa ta fi so. Ta DJ Cuppy ta zo a launin hoda, ta Temi ta zo a launin ruwan kasa sai ta Tolani da ta zo a launin bula.

Cike da annashuwa da farin ciki ‘yan matan suka garzaya kafar sada zumuntar zamani ta Instagram, inda suka wallafa hotunansu tare da saƙon godiya ga mahaifinsu.

Katafaren gidan mawaƙiya Rihanna da ke birnin London wanda ta kwashe kusan shekaru biyu da rabi ana gina shi an daga shi domin sayarwa, shafin Linda Ikeji ya wallafa.

Za a siyar da katafaren gidan a kan pam miliyan 32 wanda ya yi daida da Naira biliyan 14, shafin Linda Ikeji ya wallafa.

Gidan mai ɗakin kwana takwas yana nan a St Johns, yana da ƙofofi biyar manya tare dakin wanƙa mai kamar wurin gyaran jiki tare da katafaren lambu.

Katafaren gidan da ke birnin London na da wurin adana motoci har 10, wurin motsa jiki da manyan ɗakunan nishaɗi biyu tare da madafi katafare.

An fara gina gidan a 1844 wanda ya zama mallakin Daniel Francis, babban ɗan kasuwar lu’u-lu’u. Fitaccen magini William Holme Twentyman ne ya gina.

By ukarofi