Rasha ta samar da sabon rigakafin cutar daji

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Masana kimiyya a ƙasar Rasha sun ƙirƙiro sabon maganin rigakafin cutar daji wanda a yanzu ya kai matakin da za a iya amfani da shi kan marasa lafiya.

Hukumar Kula da Lafiya da Ilimin Halittu ta Tarayyar Rasha (FMBA), ta sanar da cewa, asibitoci za su fara amfani da sabon rigakafin, bayan amincewa da shi.

Shugabar FMBA, ɓeronika Skɓortsoɓa, ta bayyana hakan a taron tattalin arziki na Gabas, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Rasha, TASS ya ruwaito.

Maganin rigakafin, mai suna Enteromiɗ, ya dogara ne da fasahar mRNA — irin wacce aka yi amfani da ita a wasu magungunan rigakafin COɓID-19.

Madadin amfani da kwayar cuta da aka raunana, maganin rigakafin mRNA yana koya wa kwayoyin halittar jikin mutum su samar da sinadarin da ke haddasa maganin cutar daji.

Skɓortsoɓa ta ce, an samar da maganin rigakafin, bayan bincike na shekaru da dama, ciki har da gwajin farko na shekaru uku da ake buƙata.

Gwajin ya nuna cewa maganin yana da aminci har ma da tasiri ga marasa lafiya, kuma yana saurin yin aiki, a kan cutar daji.

A wasu lokuta, tsiron cutar daji na raguwa a hankali da kashi 60 zuwa 80, ya danganci irin nau’in cutar dajin.

Masu bincike sun kuma lura da yadda tsawon rayuwar mutanen da aka yi wa gwajin ya karu, inji rahoton India Today.

Wani muhimmin abu game da sabon maganin rigakafin shi ne cewa za a tsara shi ga kowane marar lafiya, daidai da RNA na mutum. Ana ɗaukar maganin a matsayin wani sabon ci gaba a fannin lafiya.

Masana kimiyya a Rasha sun ce yanzu za a iya fara amfani da wannan rigakafi ga mutane a asibitoci.

An ce, za a fara gwajin maganin ne a kan masu cutar daji ta hanji, wanda ke nufin cutar daji ta babban hanji.

Ana kuma ci gaba da aiki kan maganin cututtukan glioblastoma, wata cutar daji ce mai saurin girma a kwakwalwa, da kuma wasu nau’ikan cutar daji ta melanoma (cutar daji ta fata mai tsanani), ciki har da cutar melanoma ta ido.

An sanar da hakan ne a yayin babban taron tattalin arziki na Gabas karo na 10 a ɓladiɓostok, wanda ya samu halartar baki sama da 8,400 daga ƙasashe sama da 75.

By ukarofi