Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Kocin Wolves Julen Lopetegui ya bar ƙungiyar, inda tsohon kocin Bournemouth Gary O’Neil zai maye gurbinsa.
Wolves ta ce, ta daɗe da fahimtar cewa Lopetegui, mai shekaru 56, yana son barin ƙungiyar.
Ƙungiyar ta kuma ce dukkan vangarorin biyu sun amince da savanin ra’ayi kan wasu batutuwa kuma sun amince cewa kawo ƙarshen kwantiraginsa cikin aminci shi ne mafita mafi kyau”.
Wolves ta sanar da barin kocin ɗan Sifaniya kwanaki uku kafin a fara gasar firimiya, inda za su kara da Manchester United ranar Litinin.
Kulob ɗin ya ce, “an ci gaba da tattaunawa a cikin ‘yan makonnin nan, don bai wa kulob ɗin lokacin neman wanda zai maye gurbin Lopetegui da ma’aikatansa don tabbatar da cewa ‘yan wasa na cikin kyakkyawan yanayi don sabuwar kakar wasa.
An fahimci cewa an rufe yarjejeniyar rabuwa tun lokacin da aka yi wasan sada zumunta da Celtic a watan jiya, amma Lopetegui ya amince ya ci gaba da ba da lokaci don nemo wanda zai maye gurbinsa.
An ɗauki ‘yan takara da dama a matsayin waɗanda za su maye gurbin Lopetegui amma O’Neil mai shekaru 40 ya burge shugabannin kuma ana sa ran za a tabbatar da shi a matsayin sabon kocin ranar Laraba.
O’Neil ya jagoranci Bournemouth a gasar firimiya a kakar wasan da ta wuce, inda ta ƙare a matsayi na 15, amma an kore shi a watan Yuni kuma aka maye gurbinsa da Andoni Iraola, wanda ya jagoranci ƙungiyar Rayo Vallecano ta Spaniya zuwa matsayi na 11 a gasar La Liga a bara.