Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Rundunar ‘yan sanda a Jihar Nassarawa ta tabbatar da cewa ‘yan bindiga sun ɗauke Sarkin Gurku da iyalinsa.
Rundunar ta ce da misalin ƙarfe goma na dare, maharan, waɗanda ake zargin masu satar mutane ne ɗauke da bindigogi suka kutsa fadar mai martaba Sarkin Gurku, mai daraja ta ɗaya, Alhaji Jibrin Mohammed, bayan sun kaikaici lokacin da aka watse daga fada, wadda ke da tazarar kilomita goma da marabar Gurku da ke jikin babbar hanyar da ta tashi daga Abuja ta dangana da Keffi, inda suka tafi da shi da mai ɗakinsa.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar ta Nasarawa, Rahman Nansel, ya ce an yi wa rundunar ‘yan sanda kiran neman ɗauki a ranar 6 ga watan Agusta, cewa wasu da ake zargin masu satar mutane ne sun kai samame fadar mai martaba sarkin Gurku.
Nan da nan kwamishinan ‘yan sanda ya tura jami’ansa zuwa fadar tare da haɗin gwiwa da ‘yan banga.
Suna isa suka tarar an sace sarkin da iyalinsa, kuma ba a san inda aka tafi da su ba. An karaɗe dazukan da ke kewaye amma ba a yi nasarar samun su ba.“
Kakakin ‘yan sandan ya ce jami’ansu sun bazama, suna ƙoƙarin gano mavoyar ‘yan bindigan don ceto basaraken da mai ɗakin nasa.
Jihar Nasarawa na maƙwabtaka da jihohi da dama da ke fama da ƙalubalen da ya shafi tsaro, ciki har da Binuwai da Filato da Kaduna da Kogi da kuma Abuja, babban birnin tarayya.
Ko a watan jiya, gwamnan jihar Abdullahi Sule ya nuna damuwa game da yadda miyagun da aka fatattaka a jihohi maƙwabta ke kwarara jiharsa. Har ma ya buƙaci hedikwatar tsaron Nijeriya da ta taimaka wajen daƙile miyagun.