Wulowulo: An samu ɓullar sabuwar ƙungiyar ta’addanci mai alaƙa da Boko Haram a Arewacin Nijeriya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

An samu bayyanar wata sabuwar ƙungiyar ta’addanci mai suna ‘Wulowulo’ a shiyyar Arewa ta Tsakiya a Nijeriya.

Gwamna Abdullahi Sule na Jihar Nasarawa ne ya bayyana haka a yayin taron masu ruwa da tsaki a harkar tsaro a Lafiya, babban birnin jihar.

Ya yi gargaɗin cewa rahotannin sirri sun bayyana ƙungiyar a matsayin reshe ne na Boko Haram, wadda ke buƙatar ɗaukar matakin gaggawa, kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

Ya ce, tuni ta fara kafa sansani a yankunan shiyyar musamman a Jihar Kwara, wanda hakan tashin hankali ne ga tsaron al’umma da ma ƙasa baki ɗaya.

Gwamna Sule ya ƙara da cewa, wasu daga cikin ƙungiyoyin ta’addanci daga sassan Nijeriya sun fara bazuwa a jiharsa, yana mai shaida wa jami’an cewa ya zama wajibi a ɗauki matakin daƙile ayyukansa tun kafin su yi ƙarfi a shiyyar.

Ya cigaba da cewa, “kamar yadda kuka sani, wannan sabuwar ƙungiyar ta Wulowulo, wadda tsagi ce ta Boko Haram, ta fara samun wajen zama a shiyyar Arewa ta Tsakiya. Muna da buƙatar tabbatar da ɗaukar wasu matakai na ko da kar mu bari ta shigo cikin jharmu ne.”

Ya ƙara da cewa, ƙungiyar Lakurawa, wadda da a jihohin Kebbi da Sakkwato aka san ta, yanzu ta zama babbar matsalar a Kwara, lamarin da ke ƙara zama barazana ga yankunan ƙasar nan.

By Babaji