Kotu ta yanke masa hukuncin shekaru 14 bisa yi wa ‘yar shekara 12 fyaɗe a Kano

Spread the love

Daga USMAN KAROFI a Abuja

Wata babbar kotu a Jihar Kano mai lamba 3, ƙarƙashin jagorancin mai shari’a Farouk Lawan, ta yanke wa wani mutum mai suna Ahmed Muhammed hukuncin ɗaurin shekaru 14 a gidan yari bayan ta same shi da laifin yi wa yarinya ‘yar shekara 12 fyaɗe.

Rahotanni sun bayyana cewa an kama wanda ake zargin tun a shekara ta 2006, inda daga baya aka gurfanar da shi a gaban kotu kan wannan zargi.

Lauyan gwamnati, Barista Ibrahim Araf Garba, ya gabatar da shaidu huɗu yayin zaman shari’ar, yayin da wanda ake tuhumar ya musanta laifin da ake zarginsa da shi, inda ya tsaya kansa a matsayin shaida.

Bayan tantance shaidun da aka gabatar, mai shari’a Lawan ya bayyana cewa an tabbatar da laifin wanda ake tuhumar ba tare da wata shakka ba.

A hukuncin da ya yanke, mai shari’a Lawan ya bayyana cewa Ahmed Muhammed zai shafe shekaru 14 a gidan yari ba tare da wani zaɓin biyan tara ba. Wannan hukunci ya zo ne a matsayin gargaɗi ga masu aikata irin wannan mummunan laifi a cikin al’umma, musamman waɗanda ke cin zarafin yara mata.

By ukarofi