Kotu ta wanke Abba Kyari kan alaƙar kuɗi da Hushpuppi, inji lauya

Spread the love

Lauyan tsararren babban jami’in ƴan sanda, DCP Abba Kyari, mai suna Hamza Suleiman, ya ce kotu ta wanke ɗan sandan daga zargin karɓar kuɗi daga ɗan damfara, Ramon Abbas da aka fi sani da Hushpuppi.

Hamza Suleiman ya ce kotun ta yi watsi da buƙatar mika Kyari zuwa Amurka tun ranar 29 ga watan Agusta, 2022, kuma har yanzu ba a ɗaukaka ƙara ba.

Ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya fitar jiya a Abuja, inda ya yi bayanin cewa hukuncin kotun yana aiki har yanzu.

A cewar Suleiman, dokar ƙasa ta tanadi cewa ba za a iya mika wani ɗan ƙasa zuwa wata ƙasa ba sai da izinin kotun ƙasa.

“Tun lokacin da kotu ta yi watsi da karar, babu wani mataki da aka kara dauka. Wannan hukunci yana nan daram bisa tsarin doka.”

Ya kuma yi watsi da rahotannin da ke cewa Kyari ya karɓi kuɗi daga Hushpuppi, yana mai cewa babu wani takamaiman hujja da ke nuna haka.”

Ya ƙara da cewa, Abba Kyari bai taɓa karɓar ko kobo daga Hushpuppi ba, haka kuma ba a taɓa mayar masa da kuɗin da ‘yan sanda suka kashe wajen binciken da Hushpuppi ya kai ba.

An fara kiran ne bayan shugaban kasar ya yi wa wasu da aka kama da manyan laifuffuka afuwa, ciki har da Maryam Sanda wadda ta halaka mijinta.

By Babaji