
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ministan Kuɗi da Tsare-tsaren Tattali, Mista Wale Edun ya tafi Ingila neman magani, wanda ake ta yaɗa jita-jita akan halin rashin lafiyarsa, kamar yadda majiyoyin gwamnati da iyalansa suka tabbatar.
Wata majiya mai ƙarfi ta ce, da fari Ministan ya je Legas ne daga Abuja a daren ranar Litinin wayewar Talata, kana daga bisani ya shiga jirgi zuwa Landon.
Haka kuma, an ruwaito cewa mambobin iyalansa huɗu ne suka masa rakiya.
Wani makusancinsa da ya bayar da ba’asin ficewar Ministan zuwa ƙasar waje a farko, ya kuma tabbatar da faruwar hakan a jiya Talata.
Gabanin ficewarsa, Fadar Shugaban Ƙasa ta ce Ministan yana samun kulawar likitocin Nijeriya.
Jami’ai sun tabbatar da cewa rashin lafiyar tasa ba ta tsananta ba kamar yadda wasu kafafen labarai suka bayyana.
