
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamnan Jihar Bayelsa, Douye Diri ya fice daga cikin babbar jam’iyyar adawa, wato PDP.
Diri ya sanar da haka ne a yau Laraba, yayin zama da wasu jami’an gwamnatinsa a gidan gwamnatin jihar da ke Yenagoa.
Matakin nasa ya samu goyon bayan ƴan majalisar dokokin guda 23 ƙarƙashin jagorancin kakakinsu, saidai gwamnan bai bayyana jam’iyyar da zai koma ba zuwa yanzu.
Hakan ya faru ne kwana ɗaya da takwaransa na jihar Inugu, Peter Mbah ya bar jam’iyyar zuwa mai mulki ta APC.
Gwamnan ya taɓa riƙe muƙamin kwamishina a jihar a lokacin da tsohon shugaban ƙasa Goodluck Ebele Jonathan yake gwamna a Bayelsa.
Haka kuma ya riƙe muƙamin babban Sakataren gwamnan tsohon gwamna Seriale Dickson da magabacinsa.
