
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Chelsea ta cimma yarjejeniya a tsakaninta da Xabi Alonso akan zama mai horar da ‘yan wasanta har na tsawon shekaru huɗu, kamar yadda wani rahoto daga David Ornstein ya bayyana.
Bayan ganawa a lokuta da dama kocin mai shekaru 44 kuma ɗan Sifaniya, zai gaji Liam Rosenior da aka sallama a Afrilu ne a muƙamin.
Wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da Chelsea ke neman sabon salo da kwanciyar hankali bayan shekaru na sauye-sauyen koci-koci da kuma rashin daidaito a sakamakon wasanni.
Xabi Alonso ya samu babban yabo a shekarun baya saboda irin tsarin wasan da yake amfani da shi, ƙwarewarsa wajen sarrafa matasan ‘yan wasa, da kuma yadda yake gina ƙungiya mai tsari da kuzari.
Rahotanni sun kuma nuna cewa Alonso yana son cikakken tasiri a harkokin ƙungiyar, musamman wajen sayen ‘yan wasa, tsarin wasa, da kuma yadda za a tafiyar da aikin gina sabuwar Chelsea.
