
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal, ya ce Peter Obi da Rabi’u Musa Kwankwaso sun bar jam’iyyar ADC ne don raɗin kansu ba saboda rikicin cikin gida ba.
Da yake magana a wata hira da gidansa talabijin na Channels a yau Juma’a, Tambuwal ya yi watsi da iƙirarin cewa akwai rikicin cikin gida a haɗakar ADC da ke ƙoƙarin zama babbar matsala gabanin zaɓen 2027.
A cewarsa, ‘yan siyasar biyu sun fice daga ADC ne domin zuwa wata jam’iyya don jarraba shurarsu acikin al’umma yayin zaɓen 2027.
A kwanan nan ne Obi da Kwankwaso tare da wasu ‘yan majalisar dokoki ta ƙasa da dama suka sauya sheƙa daga ADC zuwa NDC, matakin da ya yamutsa hazo akan zargin ko sun yi haka saboda ganin fifikon karɓuwar Atiku a jam’iyyar.
Ya bayyana cewa, babu ɗaya daga cikin mutane biyun da ya zargi jam’iyyar da nuna son kai acikin gudanar da harkokinta, don haka sun ɗauki matakin nasu ne bisa raɗin kai.
Tambuwal ya kuma kare nagartar Shugaban ADC na ƙasa, David Mark, wanda ya ce mutum ne da ke tabbatar da damawa da kowane ɓangare yayin hukunci, yana mai bayar da misali da ba Obi damar naɗa sakataren shirye-shiryen jam’iyyar.
