Yusuf Buhari ya lashe zaɓen fidda gwani na neman kujerar Majalisar Wakilai a APC

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ɗan marigayi tsohon Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, wato Yusuf Buhari, ya lashe zaɓen fidda gwani a jam’iyyar APC, domin neman takarar ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar mazaɓar Daura/Sandamu/Mai-Adua daga Jihar Katsina a zaɓen 2027.

Da yake bayyana sakamakon zaɓen, shugaban kwamitin gudanar da zaɓen fidda gwani na jam’iyyar APC na mazaɓar, Lawan Garba, ya ce Yusuf Buhari ya samu ƙuri’ 17,342, inda ya kayar da abokin hamayyarsa, Auwalu Musa Daura da ya samu ƙuri’u 480.

Wannan nasara ta tabbatar da shi a matsayin ɗan takarar APC na kujerar ɗan majalisar tarayya.

An bayyana Yusuf Buhari a matsayin wanda zai wakilci jam’iyyar APC a zaɓe mai zuwa bayan samun rinjayen ƙuri’u a zaɓen fidda gwanin da aka gudanar a ranar Asabar.

Da yake jawabi bayan nasarar, Yusuf Buhari ya ce, tabbas shi ya ci zaɓen, inda ya yi alƙawarin share wa al’ummar mazaɓarsa hawaye waken kawo musu ayyukan ci-gaba a yankunansu.

By Babaji