Rashin hukunta masu laifi na lalata tsarin kwangila – Shugaban hukumar BPP

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Shugaban Hukumar Kula da Sayen Kayayyaki ta ƙasa (BPP), Dakta Adebowale Adedokun, ya bayyana cewa rashin ɗaukar tsauraran matakai kan masu karya ƙa’idoji da kuma ƙarancin ƙwarewar jami’an saye da kwangila ne manyan matsalolin da ke kassara tsarin saye da kwangilar gwamnati a Nijeriya.

Adedokun ya bayyana hakan ne yayin wata hira da Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) a Abuja ranar Lahadi, inda ya yi bayani kan ƙalubalen da hukumar ke fuskanta da kuma matakan da ake ɗauka domin ƙarfafa gaskiya da riƙon amana a harkokin kwangilar gwamnati.

A cewarsa, tsawon shekaru ana kasa hukunta munanan halaye a tsarin bayar da kwangila, lamarin da ya samar da yanayin da ‘yan kwangila da jami’ai masu aikata ba daidai ba ke ci gaba da aikinsu ba tare da tsoron hukunci ba.

“Ba mu kasance muna hukunta munanan halaye ba. Yanzu da na fara ɗaukar mataki kan masu laifi, kowa na koke-koke,” inji shi.

Ya kwatanta tsarin Nijeriya da ƙasashen da suke da tsauraran dokokin hukunta masu laifi, yana mai cewa ɗaukar matakin ladabtarwa na da muhimmanci wajen hana asarar kuɗaɗen jama’a.

“Me ya sa idan wani ya jawo wa Nijeriya asarar kuɗi, sai mutane su ce a yi masa afuwa? Idan aka ci gaba da yin haka, babu abin da zai ƙarfafa masu yin aiki da gaskiya,” inji shi.

Babban Daraktan ya ce hukumar yanzu ta fara ɗaukar matakan tabbatar da bin ƙa’idoji, hukunta ‘yan kwangilar da suka karya doka tare da ƙarfafa masu aiki da gaskiya a fannin kwangilar gwamnati.

Adedokun ya kuma ɗora alhakin gazawar tsarin kan rashin inganta ƙwarewar ma’aikata da masu hulɗa da tsarin saye da kwangila.

“Babbar matsalar yanzu ita ce batun gina ƙwarewa. Mutane sun saba da tsohon tsarin da ake gudanar da komai ba tare da tsari ba. Yanzu saye da kwangila ya zama tsarin aiki mai bin matakai, amma zama a koya yadda ake yin sa yadda ya kamata na yi wa wasu wahala,” ya bayyana.

Shugaban hukumar ya ce Gwamnatin Tarayya ta amince tare da wallafa sabuwar manufar dakatar da ‘yan kwangila masu karya doka, wadda za ta hukunta kamfanonin da ke yin ayyuka marasa inganci ko barin ayyukan gwamnati ba a kammala ba.

Ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne ya amince da manufar a shekarar 2025, inda ta mayar da hankali musamman kan ‘yan kwangilar da ke aikata zamba ko yin aikin da bai kai ƙa’ida ba, har ma da yiwuwar saka su cikin jerin kamfanonin da aka hana hulɗa da su a duniya.

A cewarsa, ko da yake har yanzu ba a kai ga dakatar da wani kamfani a hukumance ƙarƙashin sabon tsarin ba, an riga an fara aiwatar da matakan da suka dace.

“Mun riga mun samu wasu kamfanoni da Bankin Duniya da sauran abokan hulɗar ci gaba suka dakatar. Da wannan sabon tsari, mu ma za mu hana su yin kasuwanci da gwamnati,” inji shi.

Adedokun ya bayyana cewa Ma’aikatu da Hukumomi da Cibiyoyin Gwamnati ne ke da alhakin kai rahoton ‘yan kwangilar da suka karya ƙa’ida ga hukumar BPP domin ɗaukar mataki.

“Hukumar BPP ita kaɗai ba za ta iya yin hakan ba. Dole ne hukumomin da suka bayar da kwangila su aika mana da rahoto kafin mu dakatar da kamfani,” ya ce.

Ya ƙara da cewa, sabon tsarin zai zama izina ga ‘yan kwangilar da ke barin ayyuka ko aikata damfara.

“Muhimmin abu shi ne yanzu ‘yan kwangila sun san cewa idan suka bar aiki ko suka aikata laifi, za a iya dakatar da su daga harkokin gwamnati,” inji shi.

Har ila yau, Adedokun ya bayyana cewa wasu ‘yan kwangila sun riga sun mayar wa gwamnati kuɗaɗe bayan binciken da hukumar ta gudanar ya nuna sun karɓi fiye da abin da ya dace.

“Ina da ‘yan kwangilar da suka mayar wa gwamnati kuɗi bayan rahotonmu ya nuna sun karɓi kuɗi fiye da yadda ya kamata. Idan ba ka mayar ba, za ka fuskanci shari’a,” ya yi gargaɗi.

By ukarofi