Xi Ya jaddada sake farfaɗo sa yankunan karkara yayin da ya ziyarci Shaanxi da Henan

Spread the love

Daga CMG HAUSA

A yayin ziyararsa da farko tun bayan kammala babban taron wakilan jam’iyyar Kwaminis ta ƙasar Sin (JKS) na 20, Shugaban Ƙasar Sin Xi Jinping, ya jaddada buƙatar ƙara ƙaimi ga aikin farfaɗo da yankunan ƙasar baki ɗaya, da ƙara azama wajen ganin an cimma burin zamanantar da aikin gona da na yankunan karkara da aka sanya a gaba.

Ya bayyana a yayin da ya ziyarci Yan’an dake lardin Shaanxi dake Arewa maso Yammacin ƙasar da birnin Anyang dake yankin tsakiyar ƙasar daga ranar Laraba zuwa Jumma’a cewa, ya zama tilas a ba da muhimmanci wajen raya yankunan karkara, da ƙara faɗaɗa nasarorin da ƙasar ta cimma wajen kawar da ƙangin fatara.

Bisa nasarar da ƙasar ta cimma a fannin kawar da talauci, yanzu haka a shirye ƙasar ta ke ta sake yin wani sabon zagaye na raya aikin gona da yankunan karkara, a gabar da ake ci gaba da ƙara himma wajen ciyar da yankunan ƙasar gaba yadda ya kamata.

Rahoton da aka gabatarwa babban taron wakilin JKS karo na 20, ya jaddada cewa, ƙasar Sin za ta ci gaba da sanya batun raya aikin gona da yankunan karara a gaba, da ƙara ƙaimi da faɗaɗa nasarorin da aka cimma wajen yaƙar fatara, da ƙarfafa tushen samar da abinci daga dukkan fannoni.

Mai Fassara: Ibrahim

By Editor