Yaƙin Gabas ta Tsakiya ya wuce minsharrin, inji Magatakardan Majalisar Dinkin Duniya

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Babban Magatakardan Majalisar ɗinkin Duniya, Antonio Guterres, ya yi gargaɗi mai ƙarfi cewa, yaƙin da ke ƙara ƙamari a yankin Gabas ta Tsakiya tsakanin Amurka da Isra’ila akan Iran ya riga ya “wuce gona da iri”, inda ya ƙara da cewa, ya ma wuɓe minsharrin, yana mai kira ga dukkan ɓangarorin da su dakata su bai wa diflomasiyya damar warware shi.

A wani jawabi da ya gabatar a New York a ranar Laraba, Guterres ya bayyana cewa rikicin ya zarce yadda shugabanni suka yi hasashe tun farko, inda ya ce duniya na fuskantar barazanar yaƙi mai faɗaɗa, wahalar rayuwa ga jama’a da kuma girgizar tattalin arziki a matakin duniya.

Ya ce, “Duniya na tsaye a bakin wata babbar gobara ta yaƙi, tare da ƙaruwa a wahalar ɗan Adam da kuma girgizar tattalin arziki mai zurfi.” Ya ƙara da cewa, “Lamarin ya wuce gona da iri.”

Duk da tsananin tashin hankali da ci gaba da faɗaɗar rikicin, Sakataren Janar ɗin ya jaddada cewa har yanzu akwai mafita ta hanyar tattaunawa. A cewarsa, diflomasiyya ita ce hanya mafi dacewa wajen kawo ƙarshen rikicin, yana mai cewa, “Yaƙi ba shi ne mafita ba. Dole mu nemo hanyar fita daga wannan bala’i.”

A wani mataki na ƙoƙarin dawo da zaman lafiya, Guterres ya sanar da naɗa gogaggen ɗan diflomasiyya, Jean Arnault, a matsayin wakilinsa na musamman domin jagorantar ƙoƙarin sulhu na Majalisar ɗinkin Duniya a yankin.

Ya bayyana cewa sabon wakilin zai yi aiki kai tsaye a yankin domin tallafa wa duk wani yunƙuri na sasanta rikicin, tare da tattaunawa da dukkan ɓangarorin da abin ya shafa, da kuma nazarin tasirin rikicin a fannoni daban-daban.

Guterres ya nuna damuwa matuƙa kan yadda yaƙin ya rikita yankin baki ɗaya, inda tasirinsa ke yaɗuwa zuwa sassan duniya, musamman ta fuskar kasuwannin makamashi da ke dogaro da mashigar Hormuz.

Ya jaddada muhimmancin tabbatar da ‘yancin zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigar, yana mai gargadin cewa duk wani cikas da zai daɗe yana hana wucewar jiragen ruwa a yankin na iya janyo tangarɗa ga samar da mai, gas da takin zamani a duniya.

Haka kuma, Sakataren Janar ɗin ya yi gargaɗi kan illolin tattalin arziki da za su iya biyo baya, inda ya ce kasuwanni sun riga sun shiga cikin ruɗani, yayin da ayyukan jinƙai ke fuskantar ƙuntatawa. Ya bayyana cewa mafi yawan waɗanda abin ya fi shafa su ne ƙasashe masu tasowa da ke fama da basussuka da tsadar rayuwa.

Ya kuma yi nuni da cewa tangarɗar samar da takin zamani na iya zama babbar barazana ga wadatar abinci a duniya. A cewarsa, “Idan babu taki a yau, gobe za a iya fuskantar yunwa.”

A ƙarshe, Guterres ya buƙaci Amurka da Isra’ila da su kawo ƙarshen yaƙin cikin gaggawa, tare da kira ga Iran da ta daina kai hare-hare kan maƙwabtan da ba su da hannu kai tsaye a rikicin.

By ukarofi