Ya hallaka mahaifinsa kan amfanin gona

Manhaja logo
Spread the love

Wani matashi ɗan ƙasa da shekaru 20 ya hallaka mahaifinsa kan saɓani da suka samu a tsakaninsu a gona.

Yaron ya yi wa tsohon kisan gilla ne saboda dattijojin ya yi masa tambaya a gonar a ranar Juma’a da yamma a kauyen Issele-Uku da ke Karamar Hukumar Aniocha, Jihar Delta.

Wani ganau a kauyen ya ce, “Matashin ya kashe mahaifinsa ne bayan dattijon ya bi shi gona yana tambayar dalilin da ya girbe masa amfanin gona ba da izininsa ba.

“Tambayar da tsohon ya yi masa a gonar kan dalilin girbe masa amfanin gona ba da izini ba ne ya fusata matashin ya kashe shi.

“Yaron ya yi ƙoƙarin tserewa, amma mutanen ƙauyen Ukpati suka ritsa suka damƙa shi ga ’yan sanda.

“A jawabinsa a hannun ’yan sanda ya bayyana nadamarsa bisa abin da ya aikata.”

A cewarsa, wanda ake zargin ya ce, “Shi ya same ne a gona ina aiki, yana ƙoƙarin kwace addar saboda ba ma shiri da shi.

“Da ya ɗauki adda yana ƙoƙarin ya sare ni, shi ne na sa ita ce na tare shi, sannan na buga masa itacen.

“A lokacin da zai faɗi, wayar ta faɗi ƙasa, san na ɗauke ta, ba san cewa mutuwa zai yi ba.

“Da itace na yi amfani, kuma kowa ya gani, babu komai a hannuna lokacin da na tafi gona.

“Itace na buga masa sau uku, ban san cewa abin da na yi zai yi ajalin mahaifina ba.”

Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Delta, DSP Edafe Bright, ya ce, lalle an yi haka.

By Editor