Sunak ya zama sabon Fira Ministan Birtaniya

Daga BASHIR ISAH

Rishi Sunak ya samu nasarar zama sabon Fira Ministan Birtaniya bayan da ya lashe zaɓen da jami’yyarsu ta ‘Conservative’ta gudanar.

Jam’iyyar da kanta ta ba da sanarwar hakan ranar Litinin a shafinta na Tiwita.

Yanzu dai ya tabbata cewar Sunak shi ne wanda zai gaji Liz Truss wadda ta yi murabus kwanan nan.

Sunak mai shekara 42, ya zama Fira Ministan Birtaniya na farko daga Asiya, kuma mai mafi ƙanƙantar shekaru cikin sama da ƙarni ɗaya.