Gaskiyar zance kan rashin lafiyar ƙwaƙwalwar jaruma Genevieve

Daga AISHA ASAS

Biyo bayan raɗe-raɗen da ke yawo ta sama da ƙasa kan lalurar tavin hankali da shahararriyar jaruma a masana’antar Nollywood, Genevieve Nnaji, ta ke ɗauke da ita, wanda aka ce a yanzu haka jarumar na wata asibitin mahaukata da ke Ƙasar Amurka don neman lafiya.

Wannan maganar ta samu gindin zama ne a yayin da jarumar rana tsaka ta bushi iska, ta kawar da duk wani rubutu da ke kan shafinta na Instagram, wanda ta yi da wanda aka mayar mata, baya ga haka, jarumar ta janye ra’ayinta na bi-biyar waɗanda ta ke bi a shafin, inda ta bi su ɗaya bayan ɗaya tana warware alaƙar ta su.

Wannan hukuncin da jarumar ta yanke ya zama abin ban mamaki ga mafi yawan waɗanda suka santa da ma mabiyanta a shafin na sada zumunta na Instagram. Kuma da wannan ne wasu suke ganin da walakin goro a miya, kuma ruwa ba sa taɓa tsami banza.

Akan haka ne waɗanda suka fitar da wannan maganar suka fake wurin ba wa labarin rashin lafiyar jarumar wurin zama a zukatan mutane.

Jama’a da dama sun aminta da wannan magana, duba da ƙarfi da kusancin tushe da asalin wadda ta tabbatar da wannan magana, wato ɗaya daga cikin ‘yan gida, ma’ana jaruma a masana’antar ta Nollywood kuma makusanciya ga ita Genevieve, wato Stella Dimokokorkus, inda ta bayyana a shafinta na Instagram cewa, jarumar na fama da matsalar ƙwaƙwalwa kamar yadda ake zargi.

“Na jima da sanin matsalar ƙwaƙwalwa da ta ke tare da ita, sai dai na yi gum da bakina ne har zuwa lokacin da za ta samu lafiya,” inji Stella.

Ta yi wannan maganar ne a ƙoƙarin bayyana ɓacin ranta ga ma’aikaciyar jinya da ke kula da jarumar, wadda ake zargin ita ta fara ƙyanƙyashe wannan ɓoyayen lamari. Daga ƙarshe ta nemi masoya su taya ta da addu’a don samun damar yaƙar wannan lalura da ta ke tare da ita.

A cewar ta, “jaruma Genevieve na buƙatar addu’oinku da kuma soyayyarku don samun damar yaƙar wannan matsala da ta tunkaro ta, ba wai mayar da ciwonta wata dama ta gulma da raɗe-raɗin ƙwaya ce silar ciwonta ba.”

Don haka ɗimbin masoyanta suka shiga alhini tare da aika mata addu’oinsu na fatan samun waraka. Hakan ta kasance ne dalilin shurun jarumar na ɗan lokacin da wutar wannan labarin ke cin karenta ba tare da babaka ba.

Sai dai a ‘yan kwanakinan ne jarumar ta karya azumin da ta ɗauka kan wannan labarin nata da ake ya maɗiɗi da shi, inda ta fitar da bidiyo da zai zama hujjar ƙaryata masu yi mata wannan fata tare kuma da kwantar da hankalin masoyanta.

Bidiyon dai ya bayyana jarumar a yayin da ta ke yin zane, sai dai zanen bai zama kawai zane na jin daɗi ko nishaɗi ba, zane ne da ma’abuta ilimin ƙwaƙwalwa ke amfani da shi wurin fahimtar lafiya da ƙarfin hankalin ƙwaƙwalwar ɗan adam.
Wannan zane da jarumar ke yi kawai zai bayyanar da lafiyar ƙwaƙwalwarta, hakan zai kore duk wani raɗe-raɗen taɓin hankali da ake jifar ta da shi.

Sai dai wani hanzari ba gudu ba, masu iya magana sunce idan an bi ta ɓarawo, dole a bi ta mabi sawu, ɗabi’u da halayyar da jarumar ke shimfiɗawa a ‘yan watannin baya akwai ayyar tambaya a tattare da su, domin sun ɗan saɓa wa sanannen hali da aka santa da shi.

Da wannan za a iya cewa, manuniya ta nuna ga mai hankali, ko babu hauka a tattare da jaruma Genevieve, ga alama tana fama da wata matsalar a tare da ƙwaƙwalwarta, wato damuwa, saboda kamar yadda aka ce, hali zanen dutse, ba ya canza wa sai da dalili.