N500 aka biya ni a matsayin kuɗin aikin fim ɗina na farko, inji jaruma Genny Uzoma

Daga AISHA ASAS

Sana’ar fim wata hanya ce mai matuƙar birge mafi yawa daga cikin kowacce al’umma, hanya ce da mutane ke kallo mai sauƙi ta samun kuɗi da shuhura, musamman ga mata, don haka da yawa cikin mutane ke gogoriyo wurin neman hanyar da za su samu kansu a wannan ɓangare na nishaɗantarwa, fatansu su ma a tarfa wa garinsu nono su zama tamkar wance da wane.

Sai dai ba kasafai suke tsayawa tunanin ya waɗannan da suke kallo a matsayin madubi suka kai inda suke, wane irin tsani suka taka kafin su kai wannan matsayi, sukan shiga abin gaba-gaɗi, cikin gaggawa da zaƙuwa da kai ga nasara, hakan zai sa su tabka kura-kurai da daga baya su rasa maganin warakar su, wata kila ma su ta shi a tutar babu.

Da yawa sukan yi wa ita kanta sana’ar bahaguwar fahimta, inda suke ganin wuyar su da samun maƙudan kuɗaɗe to fa ba su shiga ba ne. Wannan zai sa a lokacin da suka shiga, suka samu ƙiyasin na su bai yi daidai ga haƙiƙani ba, sai su ƙi, su juya ga wasu vangarori don samun abin da ya yi daidai da lissafin da suka yi na irin adadin kuɗaɗen da za a biya su ga aikin na su, wannan kuwa zai iya haifar da faɗawa a hannun mayaudara, musamman ma a mata, idan ba a yi hattara ba, sai a tashi a tutar babu, ba wan ba ƙanin.

Harkar fim kamar sauran sana’oi ce, da rairafe ake fara ta, inda za ka fahimci hakan ta hanyar ji daga bakin waɗanda suka zama abin sha’awa kuma suke cin moriyar harkar.

Da yawa sun bayyana irin wahalar da suka fuskanta kafin su samu kansu a inda suke, wasu sun tabbatar da ba a ma biyansu a farkon finafinansu, domin yadda aka juya abin zuwa ga su ake taimakawa, sakamakon hango kwaɗayinsu ga harkar, wasu kan ce sun jima suna aikin boyi-boyi ga masu harkar kafin su aminta su saka su, yayin da wasu suka jima suna ciyar da harkar gaba ba tare da harkar ta ba su ko na abinci ba.

Shahararriyar jaruma kuma mai shirya fim a masana’antar finfinai ta Kudu, wato Nollywood, Genny Uzoma, na ɗaya daga cikin ‘yan wasan Nollywood da ke cin duniyarsu bisa tsinke a masana’antar a yanzu, kuma tana ɗaya daga cikin waɗanda za su iya zama madubi ga waɗanda ke mafarkin tsintar kansu a duniyar nishaɗantarwa ta finafinai.

A wata tattaunawa da jaridar The Guardian ta yi da ita, jarumar ta bayyana cewa, Naira ɗari biyar kacal aka biya ta a lokacin da ta taka rawa a fim ɗinta na farko. Wannan zai iya zama manuniya da ke nuni ga masu sha’awar wannan harkar cewa, ba daga shigowa ciki ne ake zama masu kuɗi ba, kuma abincin da shahara ke ci har ta yi girma shine, haƙuri.

“Tun Ina larama, zuciyata ta kamu da soyayyar harkar fasaha da adabi. Na kasance Ina kutsa kai kan sha’anin wasan kwaikwayo a lokacin da na ke karatun sakandare. Na tava taka rawa a wasan da aka shirya da littafin ‘The Incorruptible Judge’, wanda ƙwazona a wannan shirin ya bani tabbacin Ina son zama jaruma. Don haka na shiga ƙungiyar finafinai ta Actor’s Guild of Nigeria, a lokacin Ina matashiya. Kuma na yi fim ɗina na farko mai suna ‘I Waka Pass Role’ a shekara ta 2004.

A wannan fim da na yi, an biya ni Naira 500 ne a matsayin kuɗin aikina. Sai dai duk da haka na samu kaina a matsanancin farin ciki, ganin cewa, na shigo da ƙafar dama, duma ba cewa, fim ɗin na ɗoke da gwanaye kuma shahararrun ‘yan wasa irin su, Patience Uzokwu, Ini Edo da kuma Bob Manuel.

A lokacin na fara karatu a jami’a, kuma iyayena ba su goyi bayana ba, saboda kallon abin a matsayin vata lokaci kuma hanyar da zata ɗauke hankalina daga ingantacciyar rayuwa da na fara shiryawa, amma a yau mahaifiyata ce ta farko a layin masu ba ni goyon baya da alfahari da ni.”

Jaruma Genny Uzoma haifafiyyar Jihar Enugu ce, kuma a nan ta girma, sai dai Jihar Imo ce tushenta. Ita ce shugabar Zinna Studios, kamfanin nan na shirya finafinan Kudu. Ta fito a finafinai da dama da suka samu karvuwa ga masu kallo, kamar; ‘The Shopgirl’, ‘Birthday Bash’, ‘Husbands of Lagos’, ‘our Society’, ‘Baby Shower’ da sauran su.