Bai kamata a saɓa wa ƙa’idar “Ƙasar Sin ɗaya tak a duniya” ba

Daga CMG HAUSA

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin Wang Wenbin ya bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau cewa, ya kamata a bi ƙuduri mai lamba 2758 na babban taron MƊD, a kauce wa saɓa ƙa’idar “ƙasar Sin daya tak a duniya”.

Wang Wenbin ya bayyana cewa, a ranar 25 ga watan Oktoban shekarar 1971, aka zartas da ƙuduri mai lamba 2758 yayin babban taron MƊD karo na 26, ƙudurin da ya tabbatar da mayar da dukkan haƙƙin jamhuriyyar jama’ar ƙasar Sin, da amincewa da gwamnatinta a matsayin halaltacciyar wakiliyar ƙasar Sin ɗaya tak a MƊD, kana aka bukaci wakilan hukumar yankin Taiwan da su janye daga MƊD.

Wang Wenbin ya yi nuni da cewa, a shekarun baya-baya nan, wasu mutanen Amurka sun nuna ra’ayoyi da suka sabawa ƙuduri mai lamba 2758, da yada jita-jitar wai kudurin bai daidaita matsayin yankin Taiwan ba, da yin biris da ƙa’idar “ƙasar Sin ɗaya tak a duniya”, da goyon bayan ayyukan ‘yan aware a yankin Taiwan, wanda zai kawo babbar illa ga zaman lafiya da kwanciyar hankalin yankin.

A cewarsa, babu shakka ƙasa da ƙasa ba za su amince da irin wannan aiki ba, kana yunkurinsu zai ci tura domin Sinawa suna da imani da tabbataci kan ikon mulkin ƙasar da cikakkun yankunanta.

Mai fassara: Zainab