Daga FA’IZA MUSTAPHA
Ƙasar Sin ta ce ba za ta taba tilastawa ƙasashen duniya koyi da dabaru ko manufinta na raya ƙasa ba, haka kuma ba za ta amince wata ƙasa ta ƙaƙaba mata nata tsari ba.
Haƙiƙa, ƙasar Sin ta riga ta zaɓi hanyarta ta raya ƙasa da tabbatar da tsaro da tafiyar da harkokinta na cikin gida tare kulawa da al’ummarta. Ta yi, kuma an ga irin nasarori da dimbin ci gaba da ta samu.
Ƙasashe da yankuna sun bambanta, haka ma al’adu da tsaruka, kuma a tunanina, wannan shi ya sa duniyar ta zama abun sha’awa.
Don haka, kamata ya yi bambancin dake tsakaninmu, ya zama hanya ta samu ƙarin ilimi da wadata, ba wai ta nuna wariya ko danniya ba.
Kamar yadda Hausawa kan ce, mai ɗaki, shi ya san inda yake masa yoyo, gwamnati da al’umma ne suka san ƙarfi da arzikin da kuma rauninsu, haka kuma su ne suka san yanayi da al’adun da buƙatunsu, don haka, bai dace a ce wata ƙasa daga waje ce za ta tsara musu dabarun raya kansu ba.
Kamar yadda mataimkain shugaban sashen wayar da kai na kwamitin kolin Jam’iyyar Kwaminis ta ƙasar Sin Sun Yeli ya bayyana, a shirye ƙasar Sin take ta ba ƙasashen duniya damar koyon dabarunta idan suna sha’awa, amma ba bisa tilas ba.
Ina ganin, yanzu kai ya riga ya waye, ƙasashe sun san tsarin da ya dace da su da kuma waɗanda ba su dace, haka kuma sun san mai ƙaunarsu da gaske.
Haka kuma kowa a duniya shaida ne na yadda ƙasar Sin ta gina kanta da karfin da tsari da dabarun da ta zaɓar wa kanta ba tare da danniya ko mulkin mallaka ko kwaikwayon wani ba.
Lokaci ya yi da ya kamata ƙasashen duniya su yi yaki da kokarin da ƙasashe masu ganin suna da ƙarfi ke yi, na kakaba musu irin na su tsari ko yi musu danniya.
Dole ne shugabannin ƙasashe musammam na Afrika, su rika la’akari da yanayin da suke ciki da kuma buƙatun al’ummominsu domin tsara manufofin da zai dace da su tare da ba su ikon tsaya da ƙarfarsu ba zama ‘yan amshin shata ba.
