Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano
An bayyana cewa tsadar abinci da ake fuskanta a ƙasar nan wata babbar matsala ce da ya kamata al’umma su dage da addu’o’i akai Allah ya kawo mana sauƙi.
Ɗan Saran Kano, Alhaji Gambo Muhammad ɗanpass ne ya bayyana hakan da yake zantawa da ‘yan jarida ya ce ga shi yanzu a tsaka da damina ake amma kayan da ake sa ran su sauko ba a ganin wani sauyi da sauƙi.
Ya ce amma mafita shine mu gyara zuciyoyi da mu’amalarmu da tausayin juna da dagewa da addu’oi in Allah ya yarda zai shiga al’amarin a samu rahusa ta yadda za a gudanar da rayuwa cikin kwanciyar hankali.
Alhaji Gambo Muhammad ɗanpass ya yaba da irin ƙoƙari da jami’an tsaro na ƙasar nan suke wajen fatattakar ‘yan ta’adda musamman a yankin Zamfara da Sakkwato ya yi fatan za su cigaba da samun nasara har kawar da barazanar ‘yan ta’adda.
Ɗanpass ya bayyana cewa irin iftila’i na ambaliyar ruwa da ta faru a ƙasar nan abin a tausayawa al’ummar da ta shafa ne domin a wasu ƙasashe ana tanadin zuwan irin wannan data faru a ɗauki mataki na gaggawa amma mu babu irin wannan tanadi.
Ya yi nuni da cewa kamar Maiduguri da wasu jihohi da ambaliyar ta faru ba a yi tanadin komai ba sai da ambaliyar ta auku sannan ake haɗa taimako da za agaza musu irin wannan gazawa ce babba.
“Ya kamata Gwamnatin Tarayya da na jihohi da ƙananan hukumomi su riƙa tanadin duk abinda ake ganin zai iya tunkarowa na annoba a kowane mataki tunda dama aka yi hasashe domin rashin ɗaukar matakin gaggawa na rashin tanadar komai na taimakawa wajen ƙara yawan asara idan annobar ta auku kafin a kawo taimako.”
Ɗan Saran Kano ya yi nuni da cewa a wasu ƙasashe ana share filaye ne ayi gine-gine a tanadi jiragen sama da na ruwa da za a ceci jama’a koda annobar ambaliyar ko iska zata faru,amma mu babu ko ɗaya hatta jiragen sama babu irin wannan idan ya faru zai jawo asara da yawa.
Ya ce ya kamata shugabannin ƙasar nan su riƙa samun masu basu shawara na kirki da za su faɗa musu matsalolin al’umma da yadda za su tunkaresu a yi maganinsu cikin gaggawa a yi kwamiti na shawara da za a shigo da ‘yan kasuwa sarakuna da malamai na addini da na ilimin zamani da sauran mutane masu muhimmanci domin su riƙa ba gwamnati shawara akan abinda ya dace ta yi da zai kyautata rayuwar ‘yan ƙasa.
Alhaji Gambo Muhammad ɗanpass ya jajentawa al’ummar Maiduguri bisa wannan masifa ta ambaliyar ruwa da ta samesu ya kuma yaba da irin taimako da ɗauki da mutane ke bayarwa wajen agaza musu.
