Ya kamata Gwamnatin Tarayya tallafa wa jihohi don farfaɗo da masana’antu da kamfanoni – Ɗanpass

Spread the love

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

Ɗan Saran Kano, Alhaji Gambo Muhammad Ɗanpass ya ce kuɗi da  da Gwamnatin Tarayya ta ware Naira biliyan 75 don taimakawa masu ƙananan masana’antu baya jin zai amfani ‘yan Arewa yadda yakamata domin durƙushewar da masana’antu suka yi.

Ya ce a kuɗin sai an yi da gaske Arewa za ta amfana da biliyan biyar duk Kudu ne za su fi amfana saboda masana’antun namu a cewarsa sun durƙushe, a Sharaɗa da Chalawa da Bompai ba masana’antun da yawa sun zama ba a komai.

Alhaji Gambo Ɗanpass ya ce za a yi tsari na gaskiya ake so sai a ce jihar da masana’antu suka fi durƙushewa su ya kamata a ba su bashi su tayar da masana’antun a sa ido gwamnatin jihohi da na tarayya a ga an farfaɗo da su don a samu aikin yi ga matasa. 

Alhaji Gambo Muhammad ɗanpass ya yi kira gwamnatin jihar Kano akan ta dawo da tsarin nan na hana manyan motoci shigowa gari da rana tsaka domin hakan zai rage cunkoso da ake samu.

Ya ce, “a ɗauki mataki irin wanda aka ɗauka a lokacin da jagoran Kwankwasiyya yake Gwamna ya ɗauka da sai ƙarfe 10 na dare sannan ne mayan motoci za su shigo da kaya su sauke su fita amma yanzu ba a wannan ya kamata a duba a dawo da dokar zai taimaka wajen rage cunkoso.”

By ukarofi