Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Wani mutum mai suna Yusuf Usman mai shekaru 45 ya rasu bayan ya shiga wata tsohuwar rijiya da aka mayar wurin zubar da shara a garin Kwa da ke ƙaramar Hukumar Dawakin Tofa ta Jihar Kano domin ciro wayar hannu da ta faɗa ciki.
Jami’in hulɗa da jama’a na Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, Saminu Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce sun samu kiran gaggawa da misalin ƙarfe 11:13 na safe ranar Laraba, sannan aka tura jami’an ceto zuwa wurin.
A cewarsa, lokacin da jami’an suka isa sun tarar da Yusuf Usman ya maƙale a cikin rijiyar, inda ya kasa fitowa bayan ya shiga domin ciro wayar da ta faɗa ciki.
Hukumar ta ce an samu nasarar fitar da shi daga rijiyar cikin halin suma, amma daga bisani aka tabbatar da mutuwarsa sakamakon ƙarancin iskar oɗygen da kuma zafin da ke cikin rijiyar.
An miƙa gawarsa ga shugaban unguwar Kwa, Alhaji Muktar, yayin da binciken farko ya nuna cewa hatsarin ya faru ne lokacin da yake ƙoƙarin ciro wayar da ta faɗa cikin rijiyar.
Daraktan Hukumar Kashe Gobara ta Kano, Alhaji Sani Anas, ya bukaci al’umma su rika daukar matakan kariya a kusa da rijiyoyi da wurare masu haɗari, tare da rufe rijiyoyin da ba a amfani da su domin kauce wa irin waɗannan haɗurra.
