Yadda aka kaya a muhawarar Harris da Trump 

Spread the love

‘Yar takarar Jam’iyyar Democrat Kamala Harris ta taso abokin hamayyarta na Republican Donald Trump a gaba, inda ta kai shi bango kan gazawarshi a mulki, rashin isasar lafiya, goyon bayan hana zubar da ciki, da kuma matsalolin shari’a da dama da yake fuskanta.

Harris ta bayyana hakan ne a matsayin kariya a muhawarar zaɓen shugaban ƙasa da aka gudanar a ranar Talatar da ta gabata.

Tsohuwar mai gabatar da ƙara, Harris, mai shekaru 59, ta yi nasarar juya akalar muhawarar tun daga farko, inda ta ta yi mafaka a ƙarƙashin fatar abokin karawar tata, ta hanyar riƙe makamin zahiri, wato amfani da ababen da ba zai iya musanta su ba na daga halin da yake ciki, wanda hakan ya haifar da fushin Trump, mai shekaru 78.

Haka ma, ta ja kunnen tsohon shugaban ƙasar inda ta ce mutane sukan bar taron yaƙin neman zaɓensa da wuri “saboda gujewa gafara sa ban ga ƙaho ba.”

Trump, wanda ya ji takaicin yadda Harris ta ƙarɓe fagen muhawarar ta yawan jama’ar, ya ce, “A tarukan da na yi, muna da manyan taruka, taruka mafi girma a tarihin siyasa.”

Daga nan ya bijiro da wata da’awar ƙarya game da baƙin haure da ke cin dabbobi a Springfield, Ohio, wanda ke yawo a shafukan sada zumunta kuma mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na Trump, Sanata JD ɓance ne ya ruwaito shi.

“Suna cin karnuka!” Ya faɗa, yayin da Harris ke dariyar rashin yarda.

“Mutanen da suka shigo, suna cin mage! Suna cin dabbobin mutanen da ke zaune a can,” inji Trump.

“Ka yi magana game da matsananci,” Harris ya amsa.

Kamar yadda mashawarcin ‘yar takarar ya faɗa a baya, da gangan Harris ke ƙoƙarin tunzura abokin karawarta, wanda hakan wata gadar zare ce da take saƙa masa da take fatan ya hau, don ta sa Trump ɗin ya faɗi abubuwan da za su yanyo ce-ce-ku-ce a kafafen sadarwa, wato ababen da ba su da tushe.

Yayin da ya rage makonni takwas a gudanar da zaɓen, kuma kwanaki a fara kaɗa ƙuri’a wasu jihohi, muhawarar ta kasance ƙwalin ƙwal da aka shirya.

An ba da dama mai girma ga ‘yan takarar biyu don gabatar da ƙwarewarsu ga masu kallon talabijin na daga miliyoyin masu jefa ƙuri’a.

‘Yan takarar sun yi taho-mu-gama kan shige-da-fice, da manufofin ƙasashen waje da kuma kiwon lafiya, amma muhawarar ta haska takamaiman bayanan manufofin.

Wall Street ya kasance a kan gaba yayin da muhawarar da aka sa ido sosai ta bai wa masu zuba jari ƙarin haske kan muhimman batutuwan manufofin, kamar yadda kasuwannin yin fare ke ci gaba a mara wa Harris baya.

Maimakon haka, Harris ta yi nasarar dabirta tunanin Trump, yayin da ta bar magoya bayan cike da murna. Abin ƙarin murna a wurin su, shi ne yadda wasu daga cikin magoya bayan Trump suka bayyana cewa sun aminta ta shaƙe masa wuya.

Trump ya sake nanata iƙirarin nasa na ƙarya na cewa kayen da ya sha a zaɓen 2020 ya faru ne sanadiyar maguɗi, kuma ya yi karyar cewa baƙin haure sun haddasa tashin hankali.

Marc Short ya ce “Trump ya rasa damar da za ta ci gaba da mai da hankali wajen gabatar da zargin da ake yi wa Biden-Haris kan tattalin arziki da kan iyaka, kuma a maimakon haka ya afka wa tarkon da Harris ta ɗara masa ta hanyar sako batutuwan ƙanzon kurege da suka haɗa da baƙin haure da ke cin dabbobinmu.”

Short ya yi aiki a matsayin shugaban ma’aikata na tsohon mataimakin shugaban ƙasa na zamanin Trump Mike Pence.

A ci gaba da yaƙin neman zaɓen Harris, pop megastar Taylor Swift ta shaida wa mabiyanta miliyan 283 a Instagram nan da nan bayan kammala muhawarar cewa za ta mara wa mataimakiyar shugaban ƙasa Harris da abokin takararta Tim Walz baya a zaɓen na ranar 5 ga Nuwamba.

Ta rattaba hannu akan “macen mage mai ƙurciya,” mai nuni ga kalamai masu rikitarwa da ɓance ya yi.

Masu Hasashe a Yanar Gizo, sun bayyana tasirin muhawar ga zaɓen shugaban ƙasa na 2024, wanda ya nuna yuwuwar nasarar Trump na raguwa yayin muhawarar, zuwa kashi 47% daga kashi 52. Yayin da Harris ta cira zuwa 55 daga 53 bisa ɗari na bagoya baya da take da su.

A cikin ƙwarin gwiwa da farin cikin sakamakon da muhawarar ta bayar, ƙungiyar yaƙin neman zaɓen Harris ya ƙalubalanci Trump zuwa zagaye na biyu a watan Oktoba.

Baya ga haka, Trump ya ɗauki matakin da ba kasafai ake samunsa ba na shiga cikin ɗakin ƙuri’a da ke kusa da shi, aikin da aka saba barin wa magoya bayansa, inda ya shaida wa manema labarai cewa, “Wannan ita ce muhawarata mafi kyau.”

Wasu gungun masu jefa ƙuri’a da ba su yanke shawara ba sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa har yanzu ba su da tabbacin cewa ita ce ta fi dacewa da su zaɓa.

Da aka tambaye shi game da ƙalubalentar shi da kwamitin yaƙin neman zaɓe na Harris na neman muhawara ta biyu, Trump ya gaya wa Foɗ News cewa: “Tana so ne saboda ta yi rashin nasara.”

“Dole ne in yi tunani a kai, amma idan ka ci nasara a muhawarar, ina tunanin ai bai kamata in yi ba. Me zai sa in sake yin wata muhawara?” Ya ce.

Trump, wanda ya kwashe makonni yana kaddamar da hare-hare baki kan Harris ciki har da cin mutuncin wariyar launin fata da jima’i, ya kauce wa wannan takon a farkon muhawarar amma cikin sauri ya fusata a karkashin harin Harris.

Masu shiga tsakani sun tambayi Trump game da ɗaya daga cikin waɗannan hare-haren, lokacin da ya faɗa a wani taro da wata ‘yan jarida baƙar fata a watan Yuli cewa Harris ta zama “Baƙar fata.”

“Ban damu ba,” inji shi. “Duk abin da take son zama ba ni da matsala da hakan.”

Harris, wadda ke da al’adun baƙar fata da Kudancin Asiya, ta amsa da cew, “Ina tsammanin abin takaici ne cewa muna da wanda ke son zama shugaban ƙasa wanda ya ci gaba da yin ƙoƙarin amfani da ƙabilanci don rarraba jama’ar Amirka.”

Ta soki Trump kan zargin da ake masa na bada toshiyar baki ga wata jarumar batsa da aka yi masa da kuma sauran tuhume-tuhumen da aka yi masa da kuma hannu dumu-dumu a cin.zarafi.

Trump ya musanta aikata ba daidai ba kuma ya sake zargin Harris da ‘yan Jam’iyyar Democrat da kitsa dukkan lamuran ba tare da wata shaida ba.

An fara muhawarar ne da ƙarfe 9 na dare. ET (0100 GMT ranar Laraba) tare da musabaha mai ban mamaki tsakanin abokan hamayyar biyu, waɗanda ba su taɓa haɗuwa ba. Harris ta tunkari Trump a laccar sa, inda ta gabatar da kanta da suna, a cmusabaha wadda ta kasance ta farko a muhawarar shugaban ƙasa tun bayan ta shekarar 2016.

Ganawar ta kasance mai mahimmanci musamman ga Harris, tare da ƙuri’un jin ra’ayin jama’a da ke nuna cewa fiye da kashi ɗaya cikin huɗu na masu jefa ƙuri’a suna jin ba su da masaniya game da ita. Harris ta shiga gasar ne makonni bakwai da suka gabata bayan ficewar Shugaba Joe Biden.

Cikin hikima, Harris ta kai wani hari kan abokin karawar tata, ta hanyar amfani da dokar hana zubar da ciki, inda ta yi amfani da kalamai masu taɓa zuciya ta hanyar bada misali da mata da aka yi wa fyaɗe suka samu ciki, wanda rashin adalci ne hana su zaɓi.

Ta kuma yi iƙirarin cewa Trump zai goyi bayan haramcin ƙasa. Trump ya kira wannan iƙirarin ba gaskiya ba ne amma ya ƙi ya fito fili ya ce zai yi watsi da irin wannan dokar.

Har ila yau Harris ta nemi ɗaure Trump ga Project 2025, tsarin manufofin ra’ayin mazan jiya wanda ke ba da shawarar faɗaɗa ikon zartarwa, kawar da ka’idojin muhalli da kuma sanya haramcin jigilar ƙwayoyin zubar da ciki a faɗin jihar, a tsakanin sauran manufofi da dama.

Trump ya mayar da martani cewa “ba shi da wata alaƙa” da Project 2025, duk da cewa wasu mashawartan sa na da hannu wajen ƙirƙiro shi.

Ron Bonjean, wani masanin dabarun Republican, ya ce Trump “bai taɓuka komai ba” amma ya kara da cewa har yanzu babu tabbacin nasarar Harris za ta kawo canji a tafiyar siyasar.

Kuri’ar jin ra’ayin jama’a na nuni da cewa galibin Amurkawa sun ƙuduri aniyarsu, inda suka bar ‘yan kadan daga cikin masu kaɗa kuri’a da ba su tantance ba.

‘Yan takarar sun buɗe muhawarar ne ta hanyar mayar da hankali kan tattalin arziki, batun da ƙuri’ar jin ra’ayin jama’a ta nuna goyon bayan Trump.

Harris ta kai hari kan aniyar Trump na sanya haraji mai yawa kan kayayyakin ƙasashen waje, shawarar da ta kwatanta da harajin tallace-tallace kan masu matsakaicin ra’ayi yayin da ta ke bayyana shirinta na bayar da fa’idar haraji ga iyalai da kananan ‘yan kasuwa.

Trump ya soki Harris saboda hauhawar farashin kayayyaki a lokacin mulkin Biden, kodayake ya wuce gona da iri na hauhawar farashin.

Haɓakar farashin kayayyaki, inji shi, “ya kasance bala’i ga mutane, ga masu matsakaici, ga kowane aji.”

‘Yan takarar sun kuma yi musayar ra’ayi kan yaƙin Isra’ila da Gaza da kuma mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine, ko da yake babu wani ƙarin bayani kan yadda za su nemi kawo ƙarshen kowane rikici.

Harris ta zargi Trump da kasancewa a shirye don watsi da goyon bayan da Amurka ke ba Ukraine don samun tagomashi ga shugaban Rasha ɓladimir Putin.

Muhawarar shugaban kasa ba lallai ta canza tunanin masu jefa ƙuri’a ba, amma tana iya yin tasiri sosai. Rashin aikin da Biden ya yi a kan Trump a watan Yuni ya sa shi yin watsi da yakin neman zaɓensa a ranar 21 ga Yuli.

‘Yan takarar biyu suna da alaƙa sosai a cikin jihohin bakwai da ake gwabzawa da za su yanke hukunci a zaɓen, bisa ga ƙididdigar ƙuri’un da jaridar New York Times ta tattara.

By ukarofi