
Daga BELLO A. BABAJI
A ranar Juma’a ne a Abuja, aka samu rahoton sace wata mota da aka danganta ta da ofishin Mai bai wa Shugaban ƙasa Shawara kan harkar Tsaro (ONSA), Malam Nuhu Ribaɗu, inda wasu rahotanni suka ce ɗaya ce daga cikin motocin tawagarsa.
Saidai, PRNigeria ta ruwaito cewa, an yi gwanjon motar ne mai ƙirar Toyota Hilux tsohuwar bugu ga wani jami’in ofishin NSA’n tun shekaru biyu da suka gabata.
Wani soja da ke aiki da ofishin ya ce, wani jami’i ne ya faka motar a gefen hanya a yayin sallar juma’a a babban masallacin ƙasa, wato National Mosque dake Abuja da nufin yin salla.
Ya ce, an aiki jami’in ne da motar, wanda ganin yadda lokacin sallar ta ƙarato ya sa ya tsaya a masallacin.
A sakamakon sace motar ne, jami’in ya gaggauta sanar da ƴan sanda rahoton yadda abin ya faru a ofishinsu da ke kusa. A yayin haka kuma sai jawabin ya bazu acikin al’umma.
Ya kuma ce, wani ne a ofishin ƴan sandar ya fitar da rahoton, ganin cewa an shigar da ƙarar da sunan ofishin NSA’n.
Ya ƙara da cewa, faruwar irin haka a manyan birane ba sabon abu bane, inda ya koka ga yadda ake ƙoƙarin ruɗar da al’umma game da shi.
