
Daga BELLO A. BABAJI
Shamsuddeen Bala Mohammed, wanda ɗa ne ga Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, ya ce abu ne mai wahala ace mahaifinsa ya mara wa tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar baya a yayin da ya tsaya takarar kujerar shugaban ƙasa a zaɓen shekarar 2027 da ke tafe.
Ɗan gwamnan ya bayyana hakan a wani rubutu da ya wallafa ta kafar X, a yayin mayar da martani ga kalaman wani na cewa zai so ganin Atiku da Bala a inuwa ɗaya don ceto Jam’iyyar PDP.
Ya zargi Atiku da ƙoƙarin lalata siyasar mahaifin nasa a lokacin da ya ke neman tazarce a muƙaminsa na gwamnan Bauchi da kuma yunƙurin amfani da wasu manyan a jihar wajen yaƙar sa.
Ya kuma ce, ko da Atiku ya yi nasara, babu abinda zai musu sai ƙoƙarin ramuwa ga abinda ya faru a baya, ya na mai cewa lallai babu jituwa a tsakaninsu da za ta sa su haɗu da inuwa guda.
