Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Makusantan matashiyar nan da ta yi suna bayan jan hankalin gwamnatin jihar Sakkwato kan matsalar tsaro sun tabbatar wa BBC cewa an tsince ta a wani daji na jihar Zamfara bayan ɓatan-dabon da ta yi.
Tun ranar Talata ne aka bayar da rahoton ɓatan Hamdiyya Sidi Sharif, bayan ta fita domin zuwa kasuwa, lamarin da ya sanya ta kasa bayyana a zaman kotu kan shari’ar da ake mata a ranar Laraba a Sakkwato.
A watannin baya ne dai gwamnatin jihar Sakkwato ta shigar da matashiyar ƙara a gaban kotu, bisa zargin ta da aikata laifin tunzura tayar da zaune tsaye, shari’ar da har yanzu ake gudanar da ita.
A tattaunawarsa da BBC, lauyan da ke kare Hamdiyya, Abba Hikima ya ce yanzu haka tana wani asibiti da ke ƙaramar Hukumar Bakura a jihar Zamfara “cikin mummunan yanayi.”
Ya ce ”wasu mutane ne sanye da kayan ƴansanda suka kama ta a cikin Sakkwato, daga nan suka kai ta wani gida a cikin Sakkwato, inda suka ɗan azabtar da ita, har ma suka yi mata allura.
“Bayan yi mata allurar ba ta tashi ganin kanta ba sai a tsakiyar wani daji da ke jihar Zamfara, inda ɓarayi ke kama mutane,” kamar yadda lauyan nata ya shaida wa BBC.
Ya ƙara da cewa daga dajin ne Allah ya taimaketa ta gudu tare da wani mutum , har suka kai wani ƙauye da ake kira ‘Yargeɗa.
Abba Hikima ya ce kawo yanzu matashiyar na samun kulawar likitoci da jami’an tsaro a jihar Zamfara, sai dai ya ce tana cikin mawuyacin hali.
”Ban ganta ba, amma na samu na yi magana da ita (ta waya), kuma bisa ga maganganunta za ka fahimci cewa tana cikin damuwa sosai dukka alamu tana cikin ciwo,” inji shi.
