Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Rundunar ‘yan sandan Nijeriya a jihar Jigawa, ta ce ta ceto wata tsohuwa mai shekara 80 da aka yi garkuwa da ita daga gidanta da ke ƙaramar hukumar Minjibir a jihar Kano.
BBC ta rawaito cewa Kakakin Rundunar ‘yan sandan jihar SP Lawan Adam Shiisu Adam ya ce mutanen da suka yi garkuwa da tsohuwar sun ɓoye ta a cikin wani daji na jihar Jigawa mai maƙwabtaka.
”Bayan sace tsohuwar, barayin sun tafi da ita wasu dazuka da ke tsakanin ƙananan hukumomin Garki da Sule Tankarkar, daga nan ne jami’ansu tare da haɗin gwiwar ‘yan bijilanti da na ƙungiyar ‘yan bulala suka far wa maharan, bayan ɗauki-b-daɗi kuma suka samu nasarar ceto ta.”
SP Shiisu ya ce jami’ansu sun yi nasarar kama wasu manyan ‘yanfashin daji biyar da aka jima ana nema ruwa-a-jallo.
”Daga ciki akwai wanda ma har yana tsallakawa jamhuriyar Nijar ya kuma aikata laifuka a can,” inji shi.
Ya ƙara da cewa jami’an sun ƙwato bindigogi irar AK-47 guda biyu, da ƙiarar GPM da aka fi sani da mai jigida, guda ɗaya sai wayoyin hannu da kuma babura.
