El-Rufai ba ya wakiltar SDP a tattaunawar haɗaka – Adebayo

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Social Democratic Party, SDP, a zaɓen 2023, Adewole Adebayo, ya ce tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ba shi da hurumin jam’iyyar na tattaunawa da shugabannin adawa.

Mista Adebayo ya bayyana haka ne yayin da yake watsi da rahoton da ke iƙirarin cewa El-Rufai na wakiltar SDP ne a tattaunawar haɗin gwiwa da ake yi.

El-Rufai, wanda ya fice daga jam’iyyar All Progressiɓe Congress, APC, a watan Maris, ya koma jam’iyyar SDP, yana daga cikin jiga-jigan ‘yan adawa na haɗakar ‘yan adawa da su tsige Shugaba Bola Tinubu a 2027.

Sai dai da yake magana yayin wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Channels, Mista Adebayo ya fayyace cewa shugabancin jam’iyyar ne kaɗai za ta iya jagorantar tattaunawar.

“Jam’iyyar SDP ba ta da hannu a cikin wani ƙawancen da wani ke jagoranta,” inji shi.

“Jam’iyyar SDP ƙarƙashin jagorancin Alh. Shehu Gabam da Olu Agunloye, bai ba ni wani aiki na yin haɗin gwiwa a madadinsa ba.

“Ba a ba shi wani aiki ga babban ɗan uwana, El-Rufai ba. El-Rufai ba ya wakiltar SDP a kowace ƙungiya,” inji Mista Adebayo.

Da aka tambaye shi game da yiwuwar jam’iyyar SDP ta shiga cikin kawance, tsohon dan takarar shugaban kasar ya bayyana cewa jam’iyyar na nazarin zaɓin da za ta yi da kuma tsara dabarunta.

“Jam’iyyar SDP tana jira, tana bayyana nata fahimtar yadda za ta fi dacewa za ta hadu a cire wannan mutumi ta haifar da jam’iyyar APC da shugaban ƙasa maras yi wa ƙasa hidima mai suna Bola Tinubu,” inji shi.

Ya kuma bayyana dabarun cikin gida na jam’iyyar SDP, inda ya ce, “Jam’iyyar SDP tana da tsare-tsare, kuma muna duba hanyoyi daban-daban.

“Kuma mun fahimci cewa a ƙarshen zaɓen, za mu buƙaci jam’iyyar siyasa da ta dace.”

By ukarofi