Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Taron na yini biyu da ya gudana a masaukin baƙi na Hillside da ke cikin garin Katsina ya mayar da hankali akan yadda samun bayanai zai sauƙaƙa gudanar da mulki da ƙididdiga GDP, na jihohi, da kuma gabatar da sabbin tsare-tsare na tattara bayanai.
A jawabinsa muƙaddashin gwamnan jihar Malam Farouk Lawal Joɓe ya ce tattara bayanai na da matuƙar muhimmanci wajen tsara ingantattun manufofi na gwamnati.
Joɓe wanda shi ne mataimakin gwamnan jihar ya bayyana nasarorin da gwamnatin Katsina ta samu ta ɓangaren noma, inda aka kafa cibiyar kayan noma da rabon taki da manoma wanda ta hanyar tattara bayanai da ƙididdiga ne aka samu nasarar raba su.
Shi ma a nasa jawabin shugaban hukumar ƙididdiga na ƙasa Prince Adeyemi Adeneran ya ce wannan tsari na ƙididdiga na kowace jiha a Nijeriya na da matuƙar muhimmanci ga masu zuba jari da kuma tsara manufofin gwamnati.
Ya yaba wa gwamnatin Katsina kan yadda ta rungumi tsarin tare da shirin ta faɗa ɗa ƙididdiga daga shekarun 2024 zuwa 2025.
Farfesa Saifullahi Sani Ibrahim ya yi wa mahalarta taron bayanin irin rawar da gwamnati jihar ke ba sashin ƙididdiga wanda a cewarsa ya taimaka wajen samun nasarar tsarin jihar.
Ya kuma buƙaci yin haɗin gwiwa tsakanin hukumomin ƙididdiga na jihohi da na tarayya domin tabbatar da sahihin bayanai da za su inganta ci gaban ƙasa.
Taron ya samu halartar hukumomi da ma’aikatan gwamnati na jihohi da na tarayya da masana tattalin arziki gami da ƙwararru akan ƙididdiga da bayanai.
