Yadda sabbin hare-haren Boko Haram suka sanya fargaba a Borno da Yobe 

Spread the love

Daga MUHAMMAD AL-AMIN a Damaturu 

Dangane da yadda ake samun sabbin hare-haren ƙungiyar Boko Haram a wasu sassa daban-daban a jihohin Borno da Yobe, wani sabon ƙalubale ne wanda al’umma suke fargaba a kansa, al’amarin da suka bayyana a matsayin koma baya ga harkokin tsaro, biyo bayan irin ci gaban da aka samu, wanda ya kai ga jama’a sun fara dawowa hayyacin su daga mawuyacin halin da matsalar tsaro ta jefa al’ummar yankin a baya.

Sabbin hare-haren sun yi ƙamari a yan kwanankin nan, wanda ake zargin yan ta’addan Boko Haram/ISWAP da aiwatar dasu ga wasu sansanonin sojojin Nijeriya, kai farmaki a wasu garuruwa tare da daddasa nakiyoyi da tayar da bama-bamai a wurare da hanyoyi, yin garkuwa da matafiya; ciki har da yi wa manoma da masunta kisan gilla daban-daban a cikin waɗannan jihohin. 

Dangane da haka ne, a kwanan baya, Mai Martaba Shehun Borno, Alhaji Abubakar Umar Garbai El-Kanemi, ya koka bisa ga yadda mayaƙan suke ƙoƙarin dawo da hannun agogo baya kan tabarbarewar tsaro, inda bayan yaba wa ƙoƙarin hukumomin tsaro a yaƙin da suke yi da ayyukan ta’addanci, ya jaddada buƙatar ɗaukar ƙwararan matakan daƙile yaɗuwar sabbin hare-haren ta’addanci, inda ya ce har yanzu akwai sauran rina a kaba, saboda har yanzu akwai ƙananan hukumomi uku; Guzamala, Marte, da Abadam da wasu sassan Mobbar, su na ƙarƙashin ikon Boko Haram ne.

A wancan lokacin, sojojin Nijeriya sun ƙeƙasa ƙasa, inda suka musanta batun Shehun Borno, amma bisa zahiri, akwai ƙamahin gaskiya dangane da wannan al’amari sakamakon irin yadda yan ta’addan ke cin karensu babu babbaka a waɗannan yankuna. 

Shi ma a nashi ɓangaren, mai sharhi kan ƙungiyoyin ta’addanci a Cibiyar Tony Blair, Barista Bulama Bukarti, ya ce, “A binciken da muke dashi, mun gano yadda Boko Haram suke amfani da jirage marasa matuƙa wajen kai wasu hare-hare a sansanonin sojojin Nijeriya, wanda hakan babbar barazana ce ga yaƙi da ta’addanci.” 

Ta la’akari da wannan, shima Sanata Mohammad Ali Ndume, mai wakiltar kudancin jihar Borno; ba a barshi a baya ba, inda ya tofa albarkacin bakinsa dangane da waɗannan stabbin hare-haren Boko Haram, ya bayyana al’amarin a matsayin babban abin takaici, wanda bai kamata gwamnati ta yi sakaci dashi ba. Ya ce waɗannan stabbin hare-haren da ƙungiyar take aiwatarwa a wasu yankunan jihar, musamman a sansanonin sojojin Nijeriya, ba abin a zuba ido ayi kallo ba ne- a ɗauki ingantattun matakai.

A hannu guda kuma, masana sun bayyana shirin yiwa tubabbun mayaƙan Boko Haram, waɗanda suka ajiye makamai, da cewa raguwar dabara ce, wadda bata wuce rufe ƙofa da ɓarawo ba, shirin wanda aka ce ya na ƙarƙashin Operation Safe Corridor, tare da mayar dasu cikin al’umma, bayan an sauya musu tunani.

Haka zalika kuma, sun nusar da cewa (masana) duk da wannan shirin yi wa mayaƙan afuwa, Boko Haram ba ta daina aiwatar da munanan hare-hare kan sojoji da fararen hula ba. Saboda ko a cikin watan Maris na wannan shekara (2025), Boko Haram da ISWAP sun kai hari wani sansanin soja a Borno, inda suka kashe sojoji huɗu tare da lalata makaman yaƙi, kamar yadda Kamfanin Reuters ya ruwaito. Sannan sun kai ƙarin wani hari a sansanin rundunar haɗin gwiwa ta MJTF dake Wulgo, inda suka kashe sojoji 12 suka jikkata wasu goma sha biyu.

Abin bai tsaya nan ba, inda a ranar 12 ga watan Janairun da ya gabata, ƙungiyar ta kashe manoma 40 a Dumba kusa da Baga, dake jihar Borno. Sannan kuma a ranar 12 ga watan Afrilun wannan shekara, a wani harin bam da ƙungiyar ta dasa a kan hanyar Maiduguri zuwa Damboa, ya kashe fararen hula takwas tare da jikkata ƙarin wasu 21.

Saura ƙiris ƙaramar hukumar Marte ta faɗa hannun Boko Haram

Daga cikin irin munanan hare-haren da ƙungiyar take aiwatarwa, a halin da ake ciki yanzu, ƙiris ya rage ƙaramar hukumar Marte a jihar Borno ta faɗa hannun Boko Haram, wanda baya ga ita, akwai ƙarin wasu ƙananan hukumomi da suke fuskantar barazanar sabbin hare-haren ƙungiyar a Borno da Yobe. Yayin zancen da ake akwai ƙauyukan da yan ta’adda suke iko dasu tare da ɗorawa jama’a haraji. 

A nashi martani dangane da hakan, Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya bayyana fargabar cewa saura ƙiris ƙaramar hukumar Marte, mai kimanin garuruwa 300, inda zancen da ake yi yanzu, gari ɗaya ne kawai ya rage, wanda mayaƙan Boko Haram ba su mamaye ba, ya yi gargaɗin cewa bai kamata a bari ta faɗawa a hannun yan ta’adda ba. 

Gwamnan ya yi wannan kan-da-garkin a ranar Lahadin da ta gabata, sa’ilin da ya kai wata ziyarar da ya kai yankin, inda ya roki Gwamnatin Tarayya da ta yi amfani da dukkan matakan da suka dace kuma a cikin gaggawa wajen daƙile yunƙurin Boko Haram/ISWAP ƙwace Marte.  

A wannan ziyarar da Gwamna Zulum ya kai a Marte, domin gani da ido dangane da halin da ake ciki a yankin tare da ƙoƙarin lalabo mafitar zaman lafiya mai ɗorewa. 

A tattaunawarsa da manema labaru, gwamnan ya ce ziyarar ta zo ne don karfafa gwiwar al’ummar yankin, su samu juriya, da ci gaba da haɗin kai tare da tallafawa ƙoƙarin hukumomin tsaro.  

Zulum ya ƙara da cewa, sakamakon matsalolin tsaro da yawan kai hare-hare ba ƙaƙƙautawa a baya, hakan ya tilasta zakuɗa garin Marte; shekaru huɗu da suka wuce, amma abin takaici, kwanaki uku da suka gabata, Boko Haram sun sake ɓarnata gayin, al’amarin da ya jawo jama’a sake yin gudun hijira.

Ya ce, “Kimanin mutum 20,000 sun bar Marte zuwa Dikwa; wannan adadin babbar barazana ce, saboda zaman wannan adadi a sansanonin gudun hijira, akwai fargabar yawancin matasa su karkata zuwa shiga ƙungiyoyin yan ta’adda.” In ji Zulum.  

“Wannan ƙaramar hukumar Marte ta ƙunshi garuruwa da ƙauyuka sama da 300, amma yanzu gari ɗaya kacal ya rage. Kuma muddin mu ka yi sakaci, ko shakka babu Marte zai faɗa hannun yan ta’addan, wannan abin tsoro ne, kuma ina kyautata zaton hakan ba zai kasance ba.”  

“Saboda haka, ina kira ga Gwamnatin Tarayya tare da Sojojin Nijeriya, mu haɗa kai wajen hana yuwar faɗuwar Marte zuwa ga ƙungiyar Boko Haram.” In ji shi.  

Duk da hakan, Zulum ya nuna ƙarfin gwiwarsa da cewa, mafi yawan yan gudun hijira sun fara komawa bayan wannan ziyarar da ya kai tare da yaba da ƙoƙarin hukumomin tsaro da masu aikin sa kai. 

“Alhamdulillah, mun shiga garin Marte jiya kuma mun kwana tare da taimakon Sojojin Nijeriya da masu aikin sa kai, kuma al’umma sun zauma karo na biyu. Duk da haka, addu’ar da nake yi, Allah ya sa Gwamnatin Tarayya da Sojojin Nijeriya su yi duk abin da za su iya don kiyaye wannan garin,” inji shi.  

Har wala yau kuma, Gwamnan ya sake jaddada aniyarsa na tallafawa sojojin Nijeriya a ƙoƙarinsu na dawo da zaman lafiya a faɗin jihar Borno.  

“A ɓangarena na matsayin Gwamnan jihar Borno, zan yi duk abin da zai yiwu don tallafawa jaruman sojojinmu a ƙoƙarin samun dawamamen zaman lafiya mai ɗorewa a jiharmu.” In ji shi.

Gwamna Zulum, ya yi zargin cewa wasu yan siyasa da jami’an sojojin Nijeriya suna da hannu wajen rura wutar matsalolin tsaro, ta hanyar baiwa yan ta’adda bayanan sirri tare da haɗin gwiwa da yan ta’addan Boko Haram.

“Waɗannan yan ta’adda su na da masu ba su bayanan sirri tare da haɗin gwiwa a cikin sojojin Nijeriya, da kuma a cikin yan siyasa, da kuma a cikin al’umma. Saboda haka, babban abin da za mu yi shi ne dole mu ƙarfafa hanyoyin samar da bayanan sirri na leƙen asiri don daƙile waɗannan matsaloli.” 

Sa’ilin da Gwamnan yake magana kan batun yan ta’addan da suka mika wuya, ya ce ko da yake ba duk waɗanɗa suka miƙa wuya, cewa sun gyara ba, amma mafi akasari su na bayar da gudummawa sosai.  

“Ba zan iya cewa kashi 100 na waɗanda suka miƙa wuya suna yin abin da ya dace ba, amma ina tabbatar da cewa, fiye da kaso mai yawa suna aiki mai kyau kuma ba sa shiga cikin ta’addanci.” Gwamna Zulum ya jaddada . 

Gwamnan ya sake jaddada cewa mu na buƙatar Nijeriya ta samar da sabbin dabarun yaƙi da ta’addanci domin samun dawamamen zaman lafiya, tare da daƙile hanyoyin ta’addanci.

Ya ce, “Ba za a iya kawo ƙarshen yaƙi da ta’addanci ba ta hanyar amfani da makami. Dole ne mu tabbatar cewa an aiwatar da matakan zaman lafiya ma su inganci.”  

“Abin da nake nufi da matakan zaman lafiya su ne inganta al’amurran zamantakewa, gyara harkokin siyasa da na tattalin arziki.” Gwamna Zulum ya bayyana. 

A wani rahoton da BBC Hausa ta fitar; baya ga ƙaramar hukumar Marte, akwai ƙarin wasu ƙananan hukumomi waɗanda suke fuskantar barazanar Boko Haram a jihar Borno, waɗanda suka haɗa da Bama, wanda a tattaunawar, Dr Kabir ya bayyana Bama a matsayin wuri mafi tsanani wanda hare-haren Boko Haram suka tagayyara a jihar.

Sauran sun haɗa da ƙaramar hukumar Konduga, gari ne wanda ya na ɗaya daga cikin wuraren da hare-haren Boko Haram suka yi ƙamari. Sai Gwoza, Dikwa, Askira-Uba, Damboa, Mafa da Jere duk a jihar Borno.

By ukarofi