Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta shigar da ƙara kan sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, bisa zargin ɓata suna da ta yi a gidan talabiji.
An shigar da ƙarar ne a gaban Babbar Kotun Birnin Tarayya a ranar 16 ga Mayu, 2025, inda aka saka sunan Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan a matsayin wadda ake tuhuma ita kaɗai.
Gwamnati ta tuhumi Natasha da cewa “tana sane ta ke yaɗa ƙazafin da zai iya shafar mutuncin wani”, inda ta ambaci sashi na 391 na dokar penal code, CAP 89, a dokokin tarayya, 1990. Laifin yana da hukunci a ƙarƙashin sashe na 392 na wannan doka.
A cikin jerin shaidun da za su bada shaida akanta yayin shari’a akwai; Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, da tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello.
ɗaya daga cikin tuhume-tuhumen na da nasaba da zargin Akpoti-Uduaghan, inda ta zargi shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio da tsohon gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello da yunƙurin kashe ta.
Gwamnatin Tarayya tana zargin Sanatar ne da “yaɗa ƙazafi cikin sani wanda ka iya cutar da mutuncin wani,” inji sashe na 391 na dokar Penal Code, Cap 89, a dokokin tarayya, 1990. Laifin yana da hukunci a ƙarƙashin sashe na 392 na wannan doka.
Gwamnatin Tarayya ta zargi Sanatan da cewa, a cikin hirar da aka yi da ita gidan talabijin, ta ce, “Yunƙurun kisan nata na daga cikin ganawar gaggawa da Akpabio ya yi da Yahaya Bello a daren da aka kai mata hari washegari.
