Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Matatar Man Dangote ta jaddada aniyar ta na tabbatar da daidaiton farashin man fetur, duk da cewa farashin ɗanyen mai na ci gaba da tashi a duniya.
Sanarwar hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Litinin a Legas, wanda babban jami’in kula da harkokin kasuwanci na kamfanin Anthony Chiejina.
Chiejina ya bayyana cewa, kamfanin na ci gaba da rage farashin fetur a kullum, yana mai jaddada himmarsa wajen tallafa wa tattalin arzikin Nujeriya tare da sauƙaƙa wa masu amfani da ababen hawa.
“Wannan shawarar tana nuna ƙudurinmu na isar da samfuran mai masu araha kuma masu inganci.”
Chiejina ya jaddada cewa ƙoƙarin Dangote ya yi daidai da manufar Gwamnatin Tarayya ta Nijeriya ta farko, wadda ke ba da fifiko ga samar da kayayyaki a cikin gida, da kuma goyon bayan shirin sabunta ƙasa na Shugaba Bola Tinubu da nufin farfaɗo da tattalin arziki da ci gaban ƙasa.
“Tace albarkatun man fetur a cikin gida a babbar matatar ƙasa guda ɗaya na ba mu damar bayar da gudunmawa sosai ga ci gaban Nijeriya, da adana kuɗaɗen waje, da kuma ƙarfafa ƙarfin tattalin arziki.
“Muna matuƙar godiya ga Shugaba Tinubu da ya bayar da damar aiwatar da hakan ta hanyar shirin bada ɗanyen mai a Naira, wanda ya taimaka wajen rage farashin man fetur domin amfanin ‘yan Nijeriya baki ɗaya,” inji shi.
