Yadda aka yi garkuwa da ni a Romaniya – Farfesa Wole Soyinka

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Sanannen marubuci kuma wanda ya shahara a fannin ilimi a matakin duniya, Farfesa Wole Soyinka ya bayyana yadda aka yi garkuwa da shi da yi masa fashi a lokacin da ya je ƙasar Romaniya, lamarin da ya rikiɗe daga ziyarar murna zuwa iftila’i.

Rahotanni sun bayyana cewa, al’amarin ya faru da Farfesan mai shekaru 89 ne a lokacin da ya je ƙasar da nufin halartar taron Sibiu International Theater Festival (FITS), wato ɗaya daga cikin manyan tarukan wasannin kwaikwayo da makamantansu na duniya.

A wata hira da TheNEWS, Farfesan ya bayyana kaɗuwarsa bayan faruwar al’amarin a lokacin da ya rasa jirginsa a filin jiragen sama.

Ya ce, ya isa birnin Bucharest ne da misalin ƙarfe 12:10 na dare, inda akan hanyarsa ta zuwa wajen taron ne, sai direban da ya ɗauke shi ya garzaya da shi zuwa wani juji.

A nan ne aka yi masa tutsiye, inda aka buƙaci ya bada bayanan asusun bankinsa. Daga lokacin ya yi ta sanya lambobin sirri na bogi domin haifar da jinkiri da tunanin samun agaji a yayin haka.

Bayan direban da ƴan dabarsa sun gaji da jira ne sai suka jefar da shi a wajen, inda daga bisani ya samu damar zuwa masaukinsa.

Duk da cewa bai bayyana adadin kuɗaɗen da ya yi asararsu ba, ya ce hakan bai sa ya kasa aiwatar da abinda aka tsara masa ba taron.

By Babaji