Yadda ake gudanar da taron makon Shehu a Kano

Ranar 18 ga watan Janairu na shekarar 2025 aka fara gagarumin taron makon Shehu Ibrahim Niass na bana, wanda ƙungiyar Maj’mau Ahabab Sheikh Ibrahim Niass ta saba shiryawa duk shekara ƙarƙashin jagorancin shugabanta na ƙasa , Sheikh Tijjani Sani Auwalu wanda shi ne kwamishinan addinai na Kano.

Ana gudanar da Mauludin bana ne a Kano ne ƙarƙashin shugabancin Halifa Sayyadi Bashir Tijjani Usman Zangon Barebari.

Taron, wanda za a jera kwana bakwai ana yin sa, za a gabatar da takardu guda uku a rufaffen ɗakin taro na masallacin Shehu Tijjani da ke ƙofar mata.

Mataimakin gwamnan jihar, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ya halarci taron tare da jagorantar ƙaddamar da shi.

Sai zama na rana wanda Barista Habibu Ɗan Almajiri ya gabatar . Sheikh Al-Sharif Ibrahim Tahir ya gabatar da takarda mai suna ‘Sanin siyasa a wajen Sheikh Ibrahim Inyas’. Wannan maudu’i ya taɓo sanin siyasa a addinin Musulunci da sanin siyasa na duniya da sanin mu’amala da zamantakewa, da ba wa kowa haqqinsa kamar yadda ya dace a inda ya dace. Wannan maudu’i ne mai faɗin gaske wanda aka yi masa kyakkyawan nazari aka warware zare da abawa. Khalifa Aliyu Sulaiman Kila ya yi masa ta’aliki mai faɗi da gamsarwa. A zaman yamma kuwa an tattauna kan “Sheikh Muhammad Salga jagoran makarantar fiqhu na malikiyya” wanda Sheikh Abdullahi Uwais Limanci ya gabatar. Mai gabatar da takardar ya kawo tarihi da gwagwarmayar karatu da karantarwar Sheikh Muhammadu Salga da yadda ya zama fitaccen masani akan fiqhu Malikiyya a Afrika ba a iya Nijeriya kaxai ba. Wanda Sheikh Ibrahim Shehu Maihula ya yi ta’aliqi da qarin haske. Bayan an kammala Dr Sunusi Muhammad Qani ya yi jawabin godiya. A zaman safiya a rana ta biyu Sheikh Muniru Adamu Koza ya gabatar da takarda mai suna “Rawar da Shehu ya taka wajen wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali” a muhadarar Malamin ya nuna muhimmancin zaman lafiya da yadda Shehu Ibrahim ya yi kira da zaman lafiya da cire kowanne savani da tsayawa kan musulmi duka ɗan uwan musulmi ne don haka a qaunaci juna da zauna da juna lafiya. Wanda ya yi ta’aliqi a wannan muhadara shi ne Sheikh Abubakar Maɗatai. Sheikh Maɗatai ya yi ƙarin haske kan maudu’in da Sheikh Koza ya yi tare da qarin bayani mai gamsarwa kan muhimmancin zaman lafiya a wannan zamanin da cigaban da yake kawowa al’umma. A rana ta biyun da yamma an babatar da takarda mai suna “Hanyar koyarwa da jagoranci ta Sheikh Muhammadu Al-Thani Hassan Kafinga” wanda Dakta Umar Muhammad Kani inda Malam Sa’id Baƙin Ruwa ya yi masa ta’aliqi. Rana ta uku Barista Habibu Ɗan Almajiri ya gabatar da takarda mai suna “Alaƙar Shehu Ibrahim Inyas da addinin Musulunci”. Wannan takardar ta yi dogon nazari kan yadda Shehu Ibrahim ya yi hidima ga addinin Musulunci ba a iya Afrika a duniya gabaki ɗaya da yadda ya ɗora dukkan al’amuransa kan kitabu wassunna kuma irin koyarwar da duk mai da’awar Ɗariqa da Faila ya kamata ya yi kenan don koyi da Shehu Ibrahim Niass. Iman ya fito da alaƙar Sheikh Ibrahim da ilimin addinin Musulunci kwarai da gaske, inda Gwani Dakta Yusuf Ishaq Rabi’u ya yi masa ta’aliƙi.

Sai zaman rana a rana ta uku an gabatar da takarda mai suna “Bita akan Littattafan Afrika ga ‘yan Afrika” wadda Dr Atiku Balarabe Gusau ya gabatar sanna Dr Lawi Sheikh Atiku Sanka ya yi wa kyakkyawa kuma gamsasshen ta’aliqi. Zaman yamma na rana ta uku, Dr Tahir Lawan Mu’azu ne ya gabatar da takarda akan “Tarihi da ayyukan Sheikh Atiku Sanka” Marubucin ya yi kyakkyawan jawabi filla-filla kan rayuwa da gwagwarmaya da ayyukan Shehu Atiku Sanka. Manazarcin ya yi zurfaffen bincike kan wannan maudu’i. Bayan Dr Tahir Lawan Mu’azu ya gabatar da takardar sai Imam Nazifi Gambo ya yi masa ta’aliqi. A rana ta huɗu za a gabatar da takarda mai suna “Hanyar da Sheikh Ibrahim Inyas ya bi yayin kira ga Allah” wanda Dr Mustapha Kagarko zai gabatar sai kuma Imam Ɗayyib Muhammad Ɗan Almajiri zai yi ta’aliƙi. Rana ta biyu da Dr Saminu Ɗalhatu Gusau zai gabatar da takarda inda Sheikh Mustapha Maijama’a zai yi ta’aliƙi.

Za kuma a tattauna akan “Tajdidi a manhajar Sheikh Ibrahim Niass”.

A zaman yamma za a tattauna akan “Rayuwa da ayyukan Shehu Usman Maihula” wanda Dr Ibrahim Auwal Ibrahim zai gabatar inda Dr Mustapha Tijjani zai yi masa ta’aliƙi.

Rana ta biyar Iman Dr Muhammad Nazifi Bichi zai gabatar da takardarsa mai suna “Ƙwarewar Shehu Ibrahim Inyas a harshen Larabci: Tsince-tsince a Diwani” inda Malam Zubairu Madigawa zai yi ta’aliƙi. Zaman rana Farfesa Muhammad Haruna Haxeja shi zai gabatar da takarda inda Malam Ahmad Tijjani Mai Salati Indabawa zai yi ta’aliqi. Maudu’in da za a tattauna shi ne “Sheikh Ibrahim da yadda yake tu’ammali da shari’ar musulunci” Makon Shehu Rana ta shida Farfesa Abubakar Abubakar Yagawal ne zai fara gabatar da takarda da safe zai gabatar da takarda mai suna “Fahimta game da tafarkin Tijjaniya tsakanin Haqiqa da tunanin mutane” wanda Sheikh Muhammad Abdullahi Suru zai yi masa ta’alaqi. Sai kuma zama na rana wanda Dr Nasidi Abubakar zai gabatar da takarda mai suna “Shawarwarin Sheikh Ibrahim Niass ga mabiya game da ƙarfafa ƙauna a cikin Allah” inda Dr Abdullahi Mahmud Salga zai yi ta’aliqi. Sai kuma zaman yamma, inda Dr Aminu Sufi zai gabatar da takarda inda Injiniya Ali Sani Maihula zai yi ta’aliqi.

Za a rufe taron ne a ranar Juma’a 24 ga watan Janairu 2025 inda Asabar za a wayi gari da taron Mauludi na Shehu Ibrahim Inyas.

Haƙiƙa wannan mako na Sheikh Ibrahim Inyass yana ɗauke da darussa daban-daban na tarihi da gwagwarmayar malamai na ɗariƙar Tijjaniya da Failar Shehu Ibrahim da kuma almajiransa kan yaɗa addinin Musulunci da yaɗa ilimi na shari’a kamar fiqhu da ilimin lugga da zamantakewa da ƙaunar juna da muhimmancin zaman lafiya don cigaban ƙasa da al’umma.

Makon Shehu da ake gabatarwa zai ƙara samar da haɗin kan al’ummar Musulmi musamman ‘yan ɗariƙar Tijjaniya da failar Shehu.

Dubban jama’a ne suke halartar wannan zama na makon Shehu don jin karatuka da wayar da kai da bayar da ilimi da manyan malamai ke yi kullum.

Daga cikin jagororin makon Shehu akwai Sheikh Ibrahim Shehi Maihula (Shehi Shehi) da Halifan Shehu Maihula Sheikh Sani Shehu Maihula shugaban majalisar Shura ta Tijjaniya. Sai Dakta Lawi Atiku Sanka da Khalifa Sheikh Tuhami Sanka da Sayyadi Sheikh Bashir Usman Zangon Barebari da Sheikh Halifa Sukairaju Salga da da Halifa Kafinga Dr. Sunusi Ƙani da Barista Habibu Ɗan Almajiri da shugaban kwamitin yaɗa labarai Dakta Aliyu Tamasi.