Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Mazauna Millennium City, wani babban matsuguni da ke wajen birnin Kaduna, sun bayyana shiga fargaba sakamakon yawaitar sace-sacen mutane da hare-haren ’yan bindiga a yankin cikin makonnin baya-bayan nan.
Sun ce dare, wanda ya kamata ya zama lokacin hutawa, ya koma lokacin tashin hankali, yayin da suke kwanciya da fargabar ko karar abin hawa ko motsin da suka ji a wajen gidajensu na iya zama alamar sabon hari.
Fargabar ta ƙara tsananta bayan wani hari da aka kai da sanyin safiyar Talata a Nuru Suraj Estate, inda wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne suka shiga wani gida tare da yin garkuwa da kusan mutane shida, a cewar mazauna yankin.
Harin ya faru ne a daidai lokacin da mazauna Millennium City da wasu yankunan da ke kewaye da ita ke nuna damuwa kan yadda sace-sacen mutane da musayar wuta tsakanin jami’an tsaro da ’yan bindiga suka zama ruwan dare.
Wani mazaunin yankin, Kabiru Alkali, ma’aikacin gwamnati, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa maharan sun shiga gidan ne ta wata ƙofar shiga ta biyu kafin su yi garkuwa da mutanen.
Ya ce jami’an tsaro sun bi sawun maharan, lamarin da ya kai ga kuɓutar da wasu daga cikin waɗanda aka sace, yayin da sauran maharan suka tsere.
Sai dai, har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a tabbatar da adadin mutanen da aka kuɓutar ba ko kuma inda sauran waɗanda aka sace suke.
Jerin hare-hare ya ƙara jefa mazauna cikin fargaba
Mazauna yankin, ciki har da Maryam Hassan, Rakiya Umar da AbdulMajid AbdulJabbar, sun ce an samu jerin hare-hare a Babban Saura, Osibanjo Estate, Kyauta da Danhonu cikin makonnin baya-bayan nan.
AbdulMajid ya ce a farkon watan Oktoba, wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sace mutane 11 a Babban Saura.
Ya kuma ce an kai hari a Osibanjo Estate, inda maharan suka yi garkuwa da wasu mata.
A yankin Kyauta, kusa da sabon asibiti, an kuma samu wani hari da ya kai ga musayar wuta tsakanin jami’an tsaro da maharan, a cewarsa.
A ɗanhonu kuwa, wani mazaunin yankin, Awwal Sani, ya ce maharan sun sace wasu ’yan gida guda, ciki har da iyaye da ’ya’yansu biyu.
Wani mazaunin yankin ya kuma yi zargin cewa maharan kan zo ne da motar Hummer tare da babura sama da 50. Sai dai, Blueprint Manhaja ta ce ba ta iya tabbatar da wannan ikirari ba.
‘Babu ranar da ba mu jin musayar wuta’
Shugaban al’umma, Jafaru Mamman, ya ce matsalar rashin tsaro ta ƙara tsananta a yankin tun watan Satumba.
“Cikin kwanaki 40 da suka wuce, babu ranar da ba za mu ji musayar wuta a yankinmu ba,” inji shi.
Ya ce yawaitar sace-sacen mutane da abin da ya bayyana a matsayin ƙarancin jami’an tsaro sun hana mazauna yankin samun kwanciyar hankali.
“Mutane ba sa samun wani aminci. Muna kwanciya da ido ɗaya ne a buɗe. Wannan lokaci ne mai wahala ga mazauna yankin,” inji shi.
Baya ga fargabar rasa rayuka da ’yan uwa, irin waɗannan hare-hare na ƙara jefa iyalai cikin damuwa, tare da haifar da tambayoyi kan tsaron gidajensu da makomar ci gaba da zama a yankin.
Wani jami’in haɗin gwiwar jami’an tsaro da ya shiga aikin a ranar Talata ya tabbatar da cewa jami’an sun yi musayar wuta da maharan.
Ya ce jami’an tsaron sun yi nasarar fatattakar maharan, lamarin da ya tilasta musu tserewa.
Jami’in ya kuma ce wasu daga cikin maharan sun samu raunuka, sai dai bai bayyana adadinsu ba.
Harin na Talata ya faru ne ƙasa da makonni biyu bayan Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna ta sanar da kama wasu mutane takwas da ake zargi da aikata laifukan garkuwa da mutane, tare da wasu huɗu da ake zargin masu ba masu garkuwa da mutanen bayanan sirri ne.
Rundunar ta kuma ce an ƙwato bindigogin AK-47 yayin samamen.
Duk da waɗannan matakai, mazauna Millennium City na ci gaba da nuna damuwa kan tsaron yankunansu, suna kira da a ƙara ɗaukar matakan da za su taimaka wajen hana hare-hare da sace-sacen mutane.
Mazauna yankin sun ce suna son ganin jami’an gwamnati sun ziyarci al’ummarsu domin tantance girman matsalar tare da bayyana matakan da ake ɗauka don kare rayuka da dukiyoyinsu.
Mamman ya ce suna buƙatar ƙarin jami’an tsaro, sintiri na dindindin da ingantaccen tsarin tattara bayanan sirri domin gano barazanar hare-hare tun kafin su faru.
Sun kuma buƙaci samar da ingantattun hanyoyin kai rahoton gaggawa da kuma hanzarta kai ɗauki idan maharan suka shiga al’umma.
Waɗannan buƙatu na zuwa ne yayin da mazauna yankin ke nuna fargabar cewa ci gaba da kai hare-hare na iya tilasta wa wasu iyalai barin gidajensu domin neman mafaka a wuraren da suke ganin sun fi aminci.
Blueprint Manhaja ba ta yi nasarar samun bayani daga Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna kan sabon harin da ƙorafe-ƙorafen mazauna yankin ba har zuwa lokacin haɗa rahoton. Haka kuma, ba ta samu martanin gwamnatin jihar ba.
An samar da Millennium City a zamanin tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Ahmed Makarfi, a wani yunƙuri na faɗaɗa birnin da samar da gidaje ga jama’a.
Sai dai Aminu Ahmed, mai kula da harkokin filaye, ya ce rashin bin tsarin farko wajen rabon filaye da gina gidaje ya kawo cikas ga manufar samar da matsugunin yadda ya kamata.
Yayin da yankin ke ci gaba da faɗaɗa, matsalar tsaro ta zama ɗaya daga cikin manyan ƙalubalen da mazauna ke cewa suna fuskanta.
A yanzu, mazauna Millennium City na fatan gwamnati da hukumomin tsaro za su ɗauki matakan gaggawa da za su dawo musu da kwanciyar hankali, tare da samar da ingantaccen tsarin tsaro mai ɗorewa domin hana sake aukuwar irin waɗannan hare-hare.
