Daga JAMEEL GULMA a Kebbi
Rahotanni daga ƙaramar Hukumar mulki ta Jega da ke Jihar Kebbi sun bayyana tashin wata mummunar gobara da ta yi sanadiyyar ƙonewar wata asibiti safiyar Talatar da ta gabata.
Gobarar da har yanzu ba a gano musabbabin tashin ta ba, ta ƙone sashen aikin gaggawa da hatsari tare da dukkanin kayan aikin da ke ciki.
Ta ƙone babban ɗakin shan magani na asibitin ƙurmus, inda kayan duk da ke cikin ɗakunan da suka haɗa da kayan gwaje-gwaje da na ayyukan gaggawa da sauran magunguna suka ƙone.
Wani ma’aikaci a asibitin da bai so a bayyana sunansa ba ya shaida wa Blueprint Manhaja da cewa ana sa ran wutar lantarki ce sanadiyyar tashin gobarar daga wani sashe na ɗakunan aikin gaggawa.
Kwamishinan ma’aikatar lafiya, Honarabul Yunusa Musa Isma’il Birnin Yawuri ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana wa manema labarai da cewa ba shakka wannan gobarar ba ƙaramar hasara aka yi ba duk da ya ke dai ba a rasa rayuwa ko ɗaya ba.
Ya ce in Sha Allahu nan ba da daɗewa ba gwamnati za ta duba gyara wannan asibitin saboda ba mutanen garin Jega da kewaye kaɗai ta ke amfana ba, sau da yawa idan aka samu hatsari akan kawo mutane a nan domin duba lafiyarsu da gaggawa saboda kasancewarta a kan babbar hanyar da ta haɗa wannan yankin na arewacin Nijeriya da Kudanci.
Ya ja hankalin ma’aikata da su rinƙa kula da kashe kayan wutar lantarki bayan sun kare amfani da su da kuma lokacin da suka tashi daga aiki.
