Yadda Gwamna Abba ya biya wa Zainab, ‘yar Ado Bayero, da mahaifiyarta kuɗin haya a Legas

Spread the love

Daga Adnan Muktar

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya biya kuɗin hayar gida ga Zainab, ƴar marigayi tsohon Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero da mahaifiyarta, biyo bayan barazanar korar su daga gidan da su ke da aka yi a Legas.

Mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature ya ziyarci wajen da su ke a rukunin gidajen ‘Morning Side Suits’ da ke Victoria Island a ranar Talata, 25 ga watan Yuni, 2024 which a ranar ƙudinsu zai ƙare da misalin ƙarfe 3 na rana inda har ta kai ga an basu takardar ficewa daga gidan, wato ‘notice’, sannan ya gana da manajan gidajen tare da biyan kuɗin hayar.

A kwanakin baya ne, Zainab Ado Bayero wacce furodusar shirye-shiryen batutuwa ce, ta shelanta a jaridu cewa suna buƙatar taimako ita da ɗan uwanta da mahaifiyart, sannan kuma suna fuskantar ƙalubale ciki har da ƙin basu gadonsu da aka yi bayan rasuwar Mai Martaba Sarki Ado Bayero.

Bature ya ƙara da cewa, gwamnatin Kano ta shiga lamarin ne a lokacin da ta ji labarin halin da suke ciki inda yunkurinnasu zai taimaka wajen kare martabar ahalin sarautar da kuma jihar Kano.

Iyalan sun kuma yi godiya ga gwamna Abba inda suka ce taimakonnasa ya zo a lokacin da ya dace.

By Babaji