Gobara ta kama wani sashen matatar mai na Ɗangote dake kusa da Lekki jihar Legas. Masu bada agajin gaggawa sun hallara wurin kan lokaci domin kashe wutar wanda suka yi nasara.
Sai dai ba wanda ya rasa rai kuma kawo yanzu ba a son dalilin da ya jawo gobarar ba. A halin yanzu har an fara bincike domin a gano dalilin tashin gobarar.
A wata sanarwa da kamfanin matatar man ya fitar sunce ba wani abun damuwa bane, don har ma an fara bincike domin gano abinda ya faru har gobarar ta tashi.
