
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
A safiyar ranar talata ne ƴan bindiga suka kai hari wani masallaci a ƙauyen Tazame da ke ƙaramar Bungudu a Jihar Zamfara.
Jaridar ‘PRNigeria’ ta ruwaito cewa an kai harin ne a lokacin da mutane ke ƙoƙarin gudanar da sallar asuba yayinda ƴan bindigar suka buɗe wuta wa masallata inda suka kashe Ladanin masallacin da ɗan uwansa tare da raunata Limamin.
Baya ga haka ne, sun kuma yi garkuwa da wasu da dama daga cikin masallatan.
A ƴan kwanakinnan, ƴan bindiga sun kai hare-hare da dama wa masallatai da yin fashi a shaguna gami da garkuwa da mutane.
Rundunar Ƴan sandan Jihar ta aika da ƙarin jami’anta yankin don ganin an inganta tsaro tare da ceto waɗanda aka yi garkuwa da su, kamar yadda kakakin Rundunar, ASP Yazid Abubakar ya fada.
